MAJALISAR DATTIJAI TA AMINCE DA SABABBIN NADE-NADE 3 NA SHUGABA BUHARI

0
599

Daga Usman Nasidi

MAJALISAR dattijan Najeriya a karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki ta amince tare da tabbatar da sababbin nade-naden da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na wasu mambobin hukumar nan ta ci gaban yankin Neja-Delta wato, Niger Delta Development Commission a turance.

Wadanda aka amince da su din dai sun hada da Mista Chuka Ama Nwauwa daga jihar Imo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa daga jihar Ondo sai kuma Nwogu N. Nwogu daga jihar Abia .

A wani labarin kuma, babbar jam\’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya ta yi kira ga \’yan majalisar tarayyar kasar nan da su gaggauta kwace kambun shugaba Buhari tare da nada mataimakinsa a matsayin shugaban kasa biyo bayan tafiyar da ya yi zuwa birnin Landan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here