A\’isha Buhari Ce Tauraruwar Vanguard Ta Shekarar 2017

0
810
A\'iha Buhari ma na yin tallafi ga kiwon lafiya

Daga Zubair A Sada

Ga jawabin Uwargida A\’isha Buhari a wajen taron. Daraktan yada labarai na ofishinta, Malam Haruna Suleiman ya aiko mana da jawabin da hotunan.

GODIYATA ga Vanguard kan wannan kyauta wadda ban yi tsammaninta ba sam, wai an ba ni ita ne saboda ayyukan da na sanya a gabana na ciyar da rayukan al\’umma gaba, musamman a bangaren kiwon lafiya da walwalar \’yan Najeriya, musamman mata da yara da marasa galihu.

Daya daga cikin dalilan da suka sanya aka ba ni wannan kyauta shi ne tukwici ne kan wata tattaunawa da aka yi da ni wadanda wasu suke ganin na zargi gwamnatin da ni ma ina cikinta. Inason a fahimce ni, na dauki matakin nan ne saboda tunanina na adalci amma ba wai saboda rashin da\’a ko jayayya ba. ( Ai barewa ba ya gudu, matarsa/\’ya\’yansa su yi rarrafe ). An horas da ni tun fil azal in tsaya kan gaskiyata, kuma haka nake kodayaushe.

Kamar yadda mu dukanmu muka sani cewa,\’yan Najeriya suka zabi wannan gwamnatin saboda aminta da yarda da karkon mijina, kuma ina sa ran cewa, mun zo gwamnati ne domin mu yi wa Najeriya aiki daidai gwargwadon ikonmu. Bari in yi amfani da wannan dama in sanar cewa, Ina goyon bayan mijina a wannan kira na aiki kuma zan ci gaba da goyon bayansa.

Da wannan ne nake cewa na sadaukar da wannan kyauta ga jama\’ar Najeriya,musamman mata.

Na gode kwarai da wannan kyauta.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here