AN KADDAMAR DA IYAYEN KUNGIYAR YAKIN NEMAN ZABEN SHUGABA  BUHARI NA SHEKARA TA 2019

  0
  549
  Shugaba Muhammadu Buhari ne yake jaddada niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019

  Isah Ahmed, Jos

  AN gudanar da garurumin taron kaddamar da iyaye da dattawan kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammad Buhari na shekara ta 2019, ta Buhari Campaign Organisation [BCO] a babban birnin tarayya Abuja, a karshen makon da ya gabata.

  Wadanda aka kaddamar  a matsayin iyaye da dattawan  kungiyar sun hada da tsohon Gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu da dan majalisar wakilai ta tarayya Muhammad Gudaji Kazaure, da mai ba shugaban kasa shawara kuma shugaban hukumar gano kadarorin gwamnati Barista  Obno Obla da Sanata Ali Ndume da Sanata Abba Ali da Manjo Janar A.M Jibrin da Manjo A.T Umaru da Alhaji Aliko Muhammad da Alhaji Umaru Kwabo da Muhammad Indabawa da dai sauransu.

  Da yake jawabi a wajen taron shugaban dattawan kungiyar, Injiniya Marcus Gundiri ya yi kira ga iyaye da dattawan kungiyar su tashi tsaye wajen ganin cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake lashe zaben tsayar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, da kuma zaben shugaban kasa na shekara ta 2019.

  Har ila ya yi kira kan su tashi tsaye wajen wayar kan jama’a tun daga mazabu zuwa kananan hukumomi da jihohi da kasa gabaki daya kan ayyukan rasa kasa da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi wa Nijeriya.

  Shi ma a nasa jawabin shugaban kungiyar na kasa Alhaji Danladi Garba Pasali ya yi bayanin cewa shugaban Muhammad Buhari ya cika dukkan alkawarun da ya yi wa al’ummar Nijeriya, na inganta harkokin tsaro a yankin gabas ta tsakiya da yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta harkokin tattalin arzikin Nijeriya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here