Masari Ya Kaddamar Da Kwamitin Zaben Shugabannin APC

  0
  508
  Gwamna Aminu Bello Masari

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Katsina

  GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya kaddamar da kwamitin da zai gudanar da zaben shugabannin jam\’iyyar APC tun daga mazabu da kananan hukumomi.

  Da yake jawabi kafin kaddamar da kwamitin Gwamna Masari cewa ya yi an zabi shugaba da ‘yan kwamitin ne bisa cancanta.

  Alhaji Aminu Masari ya ce in za a iya tunawa an yi irin wannan zabe ne na shugabannin jam\’iyyar tun kafin a kafa gwamnati.

  Ya ci gaba da bayanin cewa a yanzu tun da suna cikin gwamnati za a iya cimma irin waccan nasara a wurin gudanar da zaben shugabannin na jam\’iyyar domin samun ingantattun shugabanni a kowane mataki a duk fadin jihar baki daya.

  \”Kwamitin zai yi aiki tare da kwamitin da za a turo daga matakin kasa domin gudanar da wannan aikin\”.

  Da yake jawabi shugaban kwamitin wanda kuma shi ne sakataren gwamnatin Jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa, godiya ya yi ga Gwamnan da ya ba shi damar yin aiki a wannan kwamitin.

  Dakta Mustapha ya kuma bayar da tabbacin yin aiki kamar yadda ya dace gwargwadon iko.

  Ya fayyace cewa shi lamarin zaben shugabannin jam\’iyya irin wannan batu ne na ‘yan cikin gida da suke tare.

  Sauran shugabannin kwamitin sun hada da babban sakatare kuma mashawarcin Gwamna a gidan gwamnati Alhaji Muntari Lawal, kwamishinan kudi, kwamishinan shari\’a, dan majalisa mai wakiltar Zango da Baure a majalisar wakilai Nasiru Sani Zangon Daura da Yusuf Barmo.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here