BARAYI SAMA DA 150 SUN TUBA SUN MIKA MAKAMANSU

0
1178
Wasu daga cikin masu tuba

 Isah Ahmed, Jos

 

AKALLA barayi da masu sayen kayan sata, sama da 150 ne suka tuba tare da mika makamansu a garin Unguwar Bawa da ke karamar hukumar Lere a jihar Kaduna,  a karshen makon da ya gabata.

Shi dai taron tubar, wanda barayin suka rika fitowa daya bayan daya, suna bayyana sunayensu tare da bayyana irin abubuwan da suka aikata a da, da kuma rantsuwa da Alkura’ani mai girma ga musulmi da rantsuwa da littafin baibul ga kiristoci kan cewa har abada sun tuba, ba za su sake aikita sata ba. An gudanar da shi ne, a karkashin jagorancin Kwamandar rundunar ‘yan sanda na shiyyar Kafanchan da ke jihar Kaduna Mista Kayode Sunday.

Da yake jawabi a wajen Kwamandan rundunar ‘yan sanda na shiyyar Kafanchan, Mista Kayode Sunday ya bayyana cewa wannan abu da wadannan mutane suka yi, na tuba daga aikata miyagun ayyukan da suke yi a da, abu ne da ake yi yanzu a duk fadin Nijeriya.

Ya ce  yanzu mutane da dama suna mika makamansu ga jami’an tsaro suna ba da gudunmawa wajen yakar aikata miyagun ayyuka a Nijeriya.

‘’Kamar yadda kuka yi rantsuwa da littafai masu tsarki cewa kun daina aikata sace- sace da miyagun ayyuka, muna fatar za ku yi aiki da wannan rantsuwa da kuka yi. Kuma muna kira ga dukkan wadanda suke rike da makamai suke aikata miyagun ayyuka a Nijeriya, su yi kokari su tuba su mika makamansu’’.

A nata jawabin Kantomar karamar hukumar Lere Misis Laraba Kantoma ta bayyana cewa ganin halin da aka shiga a wannan karamar hukuma na sace-sace da fashe-fashe da garkuwa da mutane ya sanya aka sami wasu mutane,  suka yi kokarin kafa kungiyar sa kai don yakar wannan mummunan al’amari.

Don haka ta yaba wa wannan kungiyar kan kokarin da take yi, na magance wannan mummunan al’amari.

Kantomar wadda mataimakin daraktan sashin jin dadi da walwalar jama’a na karamar hukumar Alhaji Munkaila Muhammad Galadima ya wakilta, ta yi kira ga  wadanda suka tuba su yi kokari su kama sana’o’in da doka ta yarda a yi.

Tun da farko a nasa jawabin shugaban kungiyar sa kai ta yaki da barayi da masu garkuwa da mutane da ake kira ‘yan bula Alhaji Musa Babawuro, ya bayyana cewa wadannan mutane sama da 150 da suka kunshi manya-manyan barayi da barayin shanu da awaki da masu fasa shaguna da  masu sayen kayayyakin sata dukkansu sun tuba, kuma masu makamai daga cikinsu sun mika makamansu.

Ya ce daga lokacin da suka fara gudanar da ayyukansu a yankunan kananan hukumomin Lere da Kauru da Kubau da ke jihar Kaduna, da karamar hukumar Doguwa da ke jihar Kano  zuwa yanzu sun tubar da barayi sama da 1800.

Ya mika  godiyarsu ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna kan goyan baya da hadin kan da yake ya ba su, wajen gudanar da ayyukansu na yaki da barayi da masu garkuwa da mutane.

Wasu daga cikin masu tubar da wakilinmu ya zanta da su, sun bayyana cewa sun yi wannan tuba ne tsakani da Allah kuma da yardar Allah ba za su sake komawa ga wannan mummunan aiki ba.pix

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here