Mutum 32 Suka Mutu A Tashin Tagwayen Bama-Bamai A Adamawa

0
676
Ina Sojojin Suke Ne? Boko Haram A Yobe

Saleh Shafi\’u, Daga Yola

KIMANIN mutum talatin da biyu suka rasa ransu wasu 25, suka jikkata sakamakon tashin wasu abubuwa biyu masa karfin gaske a garin Mubi ta jihar Adamawa.

Jiya Talata ne da misalin karfe daya na rana wasu mahara, sukakai harin kunar bakin wake na tada wasu bama-bamai biyu, daya cikin wani masallaci na biyun kuma a bakin babbar kasuwar Mubi.

Harin kunar bakin waken ya rutsa da mutane da dama inda majiyoyin tsaro da na jami\’an agaji ke cewa akalla mutum goma sha biyar suka mutu nan take, a rashin tagwayen bama-bamai biyu.

Wani mazaunin garin da yake kusa da inda bama-baman biyu suka tashi ya ce \”kawai sai na ji dirim!! Sai mutane na ta gudu ko ta\’ina, na ga mutanen da suka jijji ciwo ana dibe su da keken Kago Bajad wasu a motoci.

\”mutane da yawa sun mutu, amma da wuya yanzu a iya tantance wadanda suka mutu ko suka jikkata ba, amma suna da ya sa sosai\” inji gaban.

Alhaji Dalladi Chamba, ya ce \”bam din na farko ya tashi ne cikin wani masallacin \’yan gwanjo a Unguwar Yellawa, daga sabon layi, to bam da ya tashi a wannan masallacin babu wani wanda ya fita da rai, sannan daya kuma a gaba da shi bai wuce mita dari biyu tsakani ba.

\”Bam na biyun kuma ya tashi ne kusa da wani mai nama duk tsakanin bai wuce mita dari biyu ba a bakin kasuwa, dama kuma gurin a kan yawaita samun cunkoson jama\’a, to nan an samu matsala. \”Tuni jami\’an tsaro sun killace wuraren da bama-baman suka tashi, wannan ya sa da wuya a iya sani ko a tantance adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata nan take, kuma hakan sun yi domin kiyaye kada akawai wani kusa da bai tashi ba\” inji Chamba

Honarabul Musa Bello Ajayi, shi ne shugaban karamar hukumar Mubi ta arewa ya ce wannan abun bakin ciki da ya faru kullum ana gaya wa mutane su nisanci taruwa waje guda, su rika sa hankali ga irin abin da muke jiye musu tsoro.

Ya ce mutum tara sun mutu wasu goma sha hudu su jikkata a tashin  bama-baman, ya ce karamar hukumar ta samar da duk kayan aikin jinyar mutanen da suka jikkata, kuma likitoci na aiki domin ceto rayuwarsu a yanzu.\”Mutum tara mun tabbatar da sun mutu wasu kuma goma sha hudu sun jikkata, likitoci sunanan suna muso aiki a babban asibitin Mubi, karamar hukuma ta tanadi kayan aiki domin kula da marasa lafiya\” inji Ajayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here