WADANDA SUKA BATA NIJERIYA NE BA SA SON BUHARI YA CI GABA DA MULKI-DOGARA ISIYAKA

0
664
Alhaji Isiyaka Dogara Isiyaka

 Isah  Ahmed, Jos

WANI dattijo dan shekara 127, kuma tsohon malamin daji da ke zaune a garin Jos babban birnin jihar Filato, Alhaji Dogara Isiyaka ya bayyana cewa wadanda suka bata Nijeriya ne ba sa son shugaban kasa Muhammad Buhari ya ci gaba da shugabancin Nijeriya, a zabe mai zuwa na shekara ta 2019. Alhaji Dogara Isiyaka ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce duk mutumin kirki a Nijeriya ya san cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya zo da alheri a Nijeriya. Domin zuwansa ya kawar da zubar da jinin da ake yi, wanda ya yi sanadin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a Nijeriya.

Alhaji Dogara Isiyaka ya yi bayanin cewa kokarin da wasu tsofaffin janar-janar na soja da suke yi na ganin cewa shugaba Buhari bai ci gaba da mulki a Nijeriya ba, suna yin hakan ne saboda sun ga cewa hallakarsu ta zo, domin dukkansu ana zarginsu da aikata almundahana a Nijeriya. Don haka ba sa son shugaba Buhari ya ci gaba da mulki a Nijeriya.

Ya yi kira ga  al’ummar Nijeriya da su sake fitowa kwansu da kwarkwatarsu su sake zaben shugaba Muhammad Buhari a zabe mai zuwa. Domin ya ci gaba da ayyukan da ya sanya a gaba na kawo ci gaba a Nijeriya.pix

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here