Gwamnan Zamfara Ya Yaba Da Zaben APC

  0
  768
   Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
  GWAMNA Jihar Zamfara Abdul\’aziz Yari Abubakar Shatiman Mafara ya bayyana farin ciki da  yaba irin yadda ya ga \’ya\’yan jam\’iyyar APC reshen jihar suna gudanar da zaben shugabannin jam\’iyyar tun daga matakin mazabu.
  Gwamna Abdul\’aziz Yari wanda shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a mazabarsa ta Talatar Mafara da ke Jihar Zamfara.
  Ya ce hakika \’ya\’yan APC sun bi hanyar da ta dace na doka da oda kamar yadda ka\’idar jam\’iyyar take, wanda sakamakon hakan ya yi jinjinar ban girma ga shugabannin na jiha bisa irin kokarin aikin gudanar da zaben da suka yi.
  Duk bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai ba Gwamnan Zamfara shawara a kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Dosara wanda ya sanya wa takardar da ke dauke da wannan bayani hannu aka raba wa manema labarai.
  Gwamnan wanda ya kasance yana daga cikin shugabannin jam\’iyyar APC guda dari da biyar a mazabarsa Galadima a karamar hukumar Talatar Mafara ya gamsu kwarai da irin yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
  Dakta Yari Abubakar ya ci gaba da cewa irin kokari da bajintar da shugabannin jam\’iyyar suka nuna hakika zai ciyar da jihar da kuma APC gaba domin za a samu ingantaccen hadin kai.
  Dakta Yari, ya kuma gode wa shugabannin jam\’iyyar, hukumar zabe jami\’an tsaro, da dukkan hukumomi da wadanda suka bayar da gudunmawa har wannan nasara ta samu, ya kuma yi fatar Allah Ya sa a kammala zaben a dukkan mazabun 147 a jihar baki daya lafiya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here