DAGA GOBE LARABA ZA A FARA NEMAN SABON WATAN RAMADAN – Inji Sarkin Musulmi

0
743
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na Jihar Sakkwato dan takarar shugaban kasa a jam\'iyyar PDP
Daga Usman Nasidi

MAI alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar al’amurorin shari\’a ta koli, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi su nemi watan Ramdana ranan Laraba, 16 ga watan Mayu, 2018.

Mataimakin sakataren NSCIA, Farfesa Salisu Shehu, a wani jawabi da ya saki yau ya ce mai alfarma sarkin Musulmi yana taya daukacin al’umma murnar gabatowar watan Ramadana. Yana kira ga al’umma su yi amfani da wannan wata domin neman ni’imomin Allah.

Bisa da shawarar kwamitin ganin wata na kasa, Sarkin Musulmi ya yi kira ga al’ummar Musulmi su nemi watan Ramadanan 1439 da yammacin ranan Laraba, 16 ga watan Mayu 2018 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha’aban.

Idan Musulmi amintacce ya ga wata da yammacin gobe. Mai alfarma zai sanar da Alhamis, 17 ga watan Mayu 2018 a matsayin ranan 1 ga watan Ramadana.”

“ Amma idan ba a ga wata ba a ranar, za a tashi da azumi ranar Juma’a, 18 ga watan Mayu, 2018. Majalisa na kira ga Musulmi a fadin kasa su saurari sanarwar mai alfarma domin fara azumi,”

Bugu da kar, za a iya tuntubar mambobin kwamitin duba wata ta kasa.

A wata sabuwa kuma, Gwamnan jihar Sakkwato Rt.Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya kirayi daukacin musulmin Najeriya da su ci gaba da bai wa Masarautar Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya goyon baya domin ci gaba da tashi da azumin watan Ramadan rana daya a fadin kasar nan.

Gwamna Tambuwal ya ce, yin wannan da\’a da musulmin Najeriya suke yi ga wannan fada ta musulunci, biyayya ce ga Allah SWT da ya yi wa al\’umma na bin shugabanninsu. Sai ya gode wa malaman kasar nan ta yadda suke taimaka wa Mai alfarma wajen yi wa magoya bayansu bayani kan rashin biyayya ga masarautar ko mutum ya ce shi sai ya ga jinjirin watan da kansa sannan zai dauki azumi.

Ya kuma bukaci jama\’a da su dage da yin wannan bautar Allah wadda take cike da ikhlasi da wa\’azoji masu yawa ga masu arziki da talakan baki daya. sai ya nemi da a dinga sanya kasar nan a addu\’o\’in alheri musamman a wajen bude-baki da lokutan sallolin nafila na dare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here