Zaben Kananan Hukumomi An Yi Lami-lafiya A Adamawa

0
969
I G Na \'Yan Sandan Najeriya

Saleh Shafi\’u, Daga Yola

DUBBAN daruruwan mambobin jam\’iyyar APC ne suka fito domin zaban sabbin shugabannin jam\’iyyar na matakin kananan hukumom a jihar Adamawa, zaben da ya gudana lami-lafiya a daukacin sassan jihar.
Da yake yiwa \’yan jaridu bayani game da yadda zaben ya gudana Hassan Sa\’id, daya daga cikin \’yan kwamitin gudanar da zaben, yace sun gamsu da yadda jama\’a suka fito kuma suke gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Yace mafiyawan cibiyoyin kada kuri\’a a kananan hukumomin jihar an fara zaben ne misalin 10 na safe, yace a wasu cibiyoyi an samu jinkirin farawa zaben sakamakon rashin isar kayan zabe akan lokaci.
Yace \”mun ziyarci cibiyoyin kada kuri\’a da dama, mun gamsu da yadda muka tarar da jama\’a suka fito kada kuri\’a kuma munga komai na zaben yana tafiya yadda aka tsara, wannan abin farin ciki ne\” inji Hassan.
Jama\’a da dama da suka kada kuri\’a a karamar hukumar Yola ta kudu, sun bayyana zaben da cewa shine zabe mafi inganci, sukace sun kada kuri\’arsu ba tare da wata matsala ko barazana daga wasu \’yan siyasa ba.
Alhaji Iya Adamu, xaya daga masu kada kuri\’ar kuma mai goyon bayan Honarabul Aishatu Ahmad Binani, yace an gabatar musu da kwamitin gudanar da zaben a dakin taro na Lamido Zubairu dake Yola.
Yace jama\’a sun fito domin zaben shugabannin jam\’iyyar a matakin kananan hukumomi, wanda ya gudana cikin gaskiya da adalci, domin kuwa yace yanayin tsaro da kwanciyar hankali ba kamar yadda ya gudana a wasu cibiyoyin zaben gundumomi ba.
Yace jami\’an hukumar zabe INEC da jami\’an tsaro da suke lura da yadda zaben ke gudana, sun bada umurni ga masu zabe (delegates) da su shiga layi a tantancesu, \”kuma mun gudanar da zabe mun zave wadanda muke goyon baya\”.
Shima da yake magana jimkadan da kada kuri\’arsa Kakakin majalisar dokokin jihar Kabiru Mijinyawa, ya ce ya ga yadda zaben ke gudana cikin kwanciyar hankali, lamarin da ke nuni da za\’a yiwa kowa adalci.
Kakakin majalisar ya koka da halin wasu \’yan siyasar da yace haka kawai suke kirkiro da rikici da tashin hankali domin cimma wata manufa, yace \”babu wani dalin da yasa \’yan siyasa aikata haka, face neman kawo rudu da hana magoya bayansu kada kuri\’a\”.
Shugaban majalisar dokokin ya\’yi kira ga ire-iren wadannan \’yan siyasan da cewa bai kamata su na haifar da rudu tsakanin magoya bayan jam\’iyyar ba, haka kuma ya\’yi fatan wadanda suka lashe zaben zasuyi kokarin hadekan ya\’yan jam\’iyyar a jihar.
A makon da ya gabata ne jam\’iyyar APC ta gudanar da zaben shugabannin gundumominta a kasar, wanda kuma shima rahotanni sun tabbatar da cewa jama\’a sun fito domin kada kuri\’a a jihar.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here