Gwamnonin Jihohin Arewa 19 Sun Yi Rashin MD Na NNN

0
892
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na Jihar Sakkwato dan takarar shugaban kasa a jam\'iyyar PDP

Zubair Sada

GWAMNAN Jihar Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal a madadin Gwamnonin jihohi 19 da kansa da iyalansa da jama\’ar Birnin Shehu yana mika ta\’aziyyarsa ga iyalan marigayi Malam Tukur Abdurrahman Daura da ilahirin ma\’aikatan gidan jaridar NNN/GTK wadda marigayi Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Arewa, Sa Ahmadu Bello ya assasa tun zamanin dauri.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce, marigayi Malam Tukur mutum ne hziaki, ma\’aikacin jarida wanda ba ya gajiya a yayin aikinsa. Ya ce, sam Malam Tukur ba malalaci ba ne a fagen aiki, wannan kwazo nasa ne ya sanya shi ya zamo shugaban masu tattara labarai a fadar shugaban kasa a Abuja, kafin a dawo da shi a ba shi Editan jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo wadda fitaccen mawallafin nan Alhaji Abubakar Imam ya assasa ta kuma ya zamo Editanta na farko a shekarar 1939. Marigayi Malam Tukur ya zama Editan NNN Daily, sannan bayan MD na lokacin Mista Alao ya bar aiki ne Gwamnoni Arewa 19 suka nada Marigayi Malam Tukur Abdurrahman a matsayin MD ya zuwa yau karshen rayuwarsa.

\’\’ Muna rokon Allah ya jikansa ya gafarta masa kurakurensa, ya ba mu hakurin juriyar wannan babban rashi da muka yi na Manajin Daraktan kamfanin na NNN/GTK da ya yi fice a fadin kasar nan.\’\’ Inji Gwamna Tambuwal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here