Za A Yi Zabe Ranar Biyu Ga Watan Yuni A Kaduna

  0
  672
  Adawa suke da junansu koko dai siyasa ce?

   

   

   

  Za A Yi Zabe Ranar Biyu Ga Watan Yuni A Kaduna
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
  HUKUMAR zabe mai zaman kanta a Jihar Kaduna ta bayyana ranar 2/6/2018 a matsayin ranar da za a yi zaben kananan hukumomin Kaura, Jaba da na wadansu mazabu da jimillar inda za a yi zaben ya kasance guda biyu.
  Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kaduna ta bakin shugabar hukumar Dakta Saratu Audu Dikko ta tabbatar wa manema kabarai hakan a kaduna.
  Ta ce hukumar sun rigaya sun yanke shawarar gudanar da zabe a kananan hukumomi biyu da ba a yi zaben ba sannan da kuma wasu mazabun da aka soke zaben da ya gudana saboda wadansu matsalolin da suka sabawa ka\’idojin zabe.
  Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hadar da Jaba,Kaura,Kajuru yayin da Chikun da Kaduna ta kudu an bayyana zaben bai kammalu ba.
  Shugabar hukumar ta ce kananan hukumomin da aka samu nasarar kammala zabensu sun hadar da  \”Birnin-Gwari da APC ta lashe zaben da kuri\’u  34,153, Giwa APC with 57,005.
  Kamar yadda ta bayyana karamar hukumar Igabi  APC  47, 640, Ikara APC 42,312, Jama\’a PDP 45, 361, Kachia PDP 42, 242.
  Sai Kagarko APC da 63,262, Kauru PDP 24, 395, Kubau APC  47, 535, Lere APC 92,854, Kaduna ta Arewa APC 168,572.
  Kudan APC 72,021,Makarfi APC 22, 190, Sabon Gari APC da  20, 576, Zango Kataf PDP 55,643.
  Amma kananan hukumomin Sanga, Soba da Zaria APC da kuri\’u 23, 685; 40,903; 42,859

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here