MARIGAYI TSOHON SHUGABAN KASA YA CIKA SHEKARU 20 DA RASUWA                              

0
1033
Marigayi Janaral Sani Abacha

 

Daga Usman Nasidi

TAFIYA ta yi nisa Allah ya jikan mazan jiya. A jiya ne marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Sani Abacha ya cika shekaru ashirin da rasuwa.

An dai haifi Janar Sani Abacha ne a ranar 20 ga watan Satumba ta shekarar 1943 a cikin birnin Kano.

Ya yi karatunsa na Firamari a City Senior Primary School, Kano, sai ya tafi Government College, Kano, 1957-1962, Kwalejin horas da sojoji ta Kaduna Najeriya, 1962-1963.

Daga nan sai ya tafi kwalejin Horas da Sojoji ta Aldershot da ke kasar Ingila, 1963, Kwalejin horar da dakarun soji ta Warminster, ta Birtaniya 1966, 1971 Kwalejin sojoji ta Jaji da ke Kaduna, 1976, Kwalejin nazarin manufofi da tsara dabarun mulki ta Kuru, Jos, 1981.

Tun daga juyin mulki na farko a Najeriya a shekarar 1966 janar Sani Abacha ke taka rawar gani a kasar.

Allah ya amshi ran Abacha a ranar 8 ga watan Yuni shekarar 1998 yana da shekaru 54 a duniya.

Ya rasu ya bar matar aure daya Hajiya Maryam Abacha da \’ya \’ya tara mata uku da maza shida.

 

 

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here