Mashahurin Mai Kudin Najeriya Ya Ba Buhari Kyautar Motocin Alfarma 2

0
655
Shugaba Muhammadu Buhari ne yake jaddada niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019

Daga Usman Nasidi

FITACCEN mai kudin nan dan Najeriya kuma shugaban kamfanin da ke kera motoci a Najeriya na IVM Innoson wato Cif Innocent Chukwuma a ranar Alhamis din da ta gabata ya ba wata kungiyar kamfe din Buhari na zaben 2019 kyautar motoci biyu.

Motocin dai wadanda dukkan su sabbi ne samfurin SUV IVM G5 da kuma bas din Innoson samfurin IVM 5000A an mika su ne ga kungiyar Muhammadu Buhari/ Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group da ke fafutukar ganin shugaba Buhari ya zarce a 2019.

Majiyarmu ta samu labarin cewa fitaccen mai kudin dai ya bayyana kyautar motocin a matsayin wata gudummuwarsa ga shugaban kasar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here