Mata Manoma Dake Jihar Kano Suna Bada Gudummawa Wajen Wadata Kasa Da Abinci-Altine RIFAN

0
682

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

AN bayyana cewa mata manoma dake jihar kano suna bada gagarumar gudummawar su wajen wadata kasa da abinci musamman ganin yadda gwamnati mai ci take samarfa yanayi mai kyau ga fannin noma.

Wannan tsokaci ya fito ne daga shugabar matan kungiyar manoma shinkafa ta RIFAN,  Hajiya Altine Idris cikin hirar da suka yi da wakilinmu, inda ta kara da cewa mata manoma da ke sana\’ar noma a fadin jihar Kano suna kokari matuka wajen aikin gona kamar yadda ake gani a halin yanzu.

Sannan ta bayyana cewa mata maoman shinkafa sun kasance a sahun gaba wajen samar da ayyukan yi ga al\’uma tare da bude hanyoyi na dogaro da kai ganin yadda harkar noma take da riba ta kowane fanni kamar yadda mata manoma da ke jihar Kano suke gani a kasa.

Hajiya Altine Idris ta kuma yi amfani da wannan dama wajen yin godiya ta musamman ga shugabannin kungiyar RIFAN saboda kokarin da suke yi wajen bunkasa noman shikafa a jihar Kano, wanda hakan ta sanya kwalliya take biyan kusin sabulu ta wannan fuska.

Haka kuma shugabar ta sanar da cewa Nijeriya tana cimma nasarori wajen bunkasa noma da  kiwo ta fuskoki daban-daban, sannan kowa ya yarda cewa nan gaba kadan,  sana\’ar noma za ta zamo abin alfahari ga masu gudanar da ita, inda kuma ta yi kira ga ‘yan uwanta mata da su kara himma wajen aikin noma da kiwo domin kyautata zamantakewar su da kuma iyalai.

Daga karshe, Hajiya Altine Idris ta roki gwamnatin tarayya da ta yi wani motsi wajen bai wa mata manoma tallafi mai inganci wanda zai ba su kwarin gwuiwar ci gaba da aikin noma a yankunansu, sannan ta yaba wa gwamnatin jihar Kano da ma\’aikatar gona ta jihar da hukumar bunkasa noma ta KNARDA da kuma kungiyar RIFAN wadda ita ce jagorar manoman shinkafa  kamar yadda ake gani a yau.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here