Dimbin al\’ummar Jihar Zamfara Na Yin Kaura Dalilin \’Yan Bindiga Dadi

0
670
I G Na \'Yan Sandan Najeriya

Rabo Haladu    Daga Kaduna

DARURUWAN mutane na yin kaura zuwa makwabtan jihohi kamar Katsina sakamakon karuwar ayyukan \’yan bindiga.

Ban da \’yan bindiga akwai kuma matsalar masu satar mutane don neman kudin fansa.

Al\’amarin, a cewar wasu mazauna garuruwan jihar ya kai har da rana tsaka \’yan bindiga na iya zuwa su sungumi mutum zuwa daji har sai an biya kudin fansa.

Wani mazaunin karamar hukumar Shinkafi, Sulaiman Shu\’aibu Shinkafi ya shaida wa manema labarai  cewa matsalar tana neman fin karfinsu.

\”Tura ta kai bango, matsala ta taso mana, wanda tun ana yi kauyuka har an kai yau sai a shiga Shinkafi da bindigogi, da manyan makamai a dauki mutum a tafi da shi.\”daji domin neman kudin fansa .

Sulaiman Shu\’aibu Shinkafi ya kuma koka da cewa, \”Mutane na kallo ba abin da za su iya yi saboda da manyan makamai suke zuwa.\”

Rahotanni sun ce da misalin karfe daya da rabi na dare mahara suka shiga garin na Shinkafi suna harbe-harbe.

\”Sun dauki wani dan uwanmu da karfin tsiya tare da sakataren karamar hukumar Shinkafi, kuma sun tafi da su daji. Sun kuma sake daukar wani kaninmu.\”saboda ba yadda za mu yi tura ta kai bango.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here