WADANDA SUKA ZARGI RARARA BASU TAIMAKI MAWAKAN APC BA-MURTALA MAMSA

  0
  1128

  Isah Ahmed, Jos 

  Murtala Abdullahi Mamsa Jos shi ne shugaban kungiyar mawakan jam’iyyar APC [ANMPO]  reshen jihar Filato kuma   sabon mataimakin shugaban wannan kungiya  na kasa.

  A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan zargin da aka yiwa fitattacen mawakin nan, Dauda Kahutu Rarara cewa ya ci kudin kungiyar mawakan jam’iyyar APC [ANMPO]. Ya bayyana cewa wadanda suka yi wannan zargi basu taimaki mawakan jam’iyyar APC ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK; Mene ne makasudin kiran wannan taron ‘yan jarida?

  Murtala Mamsa; Makasudin kiran wannan taron ‘yan jarida shi ne kan abubuwan da suke faruwa a Kungiyarmu ta mawaKan jam’iyyar APC ta arewa[ANMPO]. Wanda ya kai har ana yunKurin  saka wasu mutane masu mutumci a cikin wannan dambarwa da take faruwa.

  Dalilin da yasa na faDi haka shi ne ana ta cece kuce kan cewa wai shugaban amintattu na wannan Kungiya ta mawakan jam’iyyar APC ta arewa [ANMPO]  Dauda Kahutu Rarara ya ci wasu kudade, wasu suna cewa naira miliyan 60 wasu suna cewa naira miliyan 100, wasu kuma suna cewa naira miliyan 180.

  Ina son na sanar da duniya cewa wannan magana ba gaskiya bace.

  Kuma tsakani da Allah Dauda Kahutu Rarara masoyinmu ne, domin idan aka cire gwamnan jihar Kaduna Malam Ahmed El-Rufa’i mawakan jam’iyyar APC basu da uban da ya wuce Rarara. Domin tun bayan da aka kafa wannan gwamnati,  babu wanda ya taba kiran  ‘yan wannan kungiya ya taimaka masu kan irin gudunmawar da suka baiwa wannan gwamnati.

  Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya yi nasa iyakar kokarin. Amma baya ga shi tun da aka gama yakin neman zave  a kasar nan, babu wanda ya sake kiran mawakan jam’iyyar APC.

  Amma daukakar da  Dauda Kahutu Rarara ya samu ta sanya yabi kowace jiha ya ce a kawo mawakan da suka baiwa  tafiyar wannan gwamnati gudunmawa. Aka hada wata kungiya wadda daga kafa wannan kungiya, zuwa yanzu mawaka  sun sami amfani kwarai da gaske.

  A tafiyar wannan kungiya mun ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i mun ga gwamnan jihar Katsina, mun ga gwamnan jihar Zamfara mun ga gwamnan jihar Adamawa.

  Abin da ya faru kan wannan dambarwa ba a yiwa gwamnan jihar Zamfara adalci ba. A ce wai gwamna ya dauki kudi naira miliyan 100, ya baiwa wani mawaki . Akwai kuskure a wannan magana.

  Da mu aka tafi wajen gwamnan jihar Zamfara muka zauna da shi Rarara Kahutu ya mike ya koka  masa cewa ya kamata a taimaki mawakan jam’iyyar APC.

  An yi wannan magana ana kokari ana bin maganar. Yanzu kuma an zo an fito da wani irin abu na son rai, damuwar kowa ita ce maganar kudin da aka ce za a bayar. Kowa ya kira Dauda Rarara sai maganar kudi. Kuma sai ya zamanto shi Rarara Kahutu shi mutum ne mai yawan harkoki a gabansa.

  Ana cikin haka sai shugaban wannan kungiya na kasa Alhaji Aliyu Ningi da Ibrahim Yala suka ce ayi bincike don a san ina ne wadannan kudade suka shiga.

  Ba ayi bincike ba kamar yadda aka ce za a yi, sai kawai muka ji a kafafon watsa labarai shi shugaban wannan kungiya Haruna Aliyu Ningi yana cewa maganar kudi ta fito.

  Kuma da aka fito da wannan magana kowa sai zagi da wanda ya kai, da wanda bai kai   ba. Ana zagin gwamna alhalin bai san wannan abu ba.Mutumin nan bai bada kudin nan ba.

   Shi ma Dauda Rarara da yazo da abin alherin nan na kafa wannan qungiya, sai ya zamana  ana zaginsa da cin mutumcinsa. Alhalin masu wannan zargi basu da hujja kan wannan zargi da suke yi.

  Don haka muka kira wannan taron ‘yan jarida domin Dauda Kahutu Rarara ba zai yi magana ba. Idan aka ji Rarara ya yi magana abu biyu ne zasu sanya shi ya yi Magana, wanda ya bashi kudi ya fito ya yi magana cewa ya bashi kudin, sai Dauda Rarara ya fito ya yi magana  ya kare kansa ko kuma idan ana son Rarara ya yi magana a taba shugaban kasa Buhari. Tun da aka fara wannan magana yau sama da mako biyu ke nan  bai ce komai ba. Amma a ‘yan kwanakin nan da ‘yan majalisa suka ce zasu tsige Buhari nan take ya fitar da waka kan wannan batu.

  Kuma kamar Abubakar Sani mun san cewa shi dan kwankwasiya ne kuma dakatar da shugaban kungiyar mawaqan jam’iyyar APC Alhaji Haruna Ningi bashi da nasaba da maganar ya yi magana da ‘yan jarida kan wannan zargi da ake yiwa Rarara.

  A bayanin da majalisar koli ta wannan kungiya tayi mana shi ne  yana takara a wata jam’iyya ba jam’iyyar APC ba.

  Kamar  shi Alhaji Ibrahim Yala akwai hotunansa da suka yi ta yawo a dandalin yanar gizo sanye da jar hula a ‘yan kwanakin nan, sakamakon wannan dambarwa. Kaga wannan yana nuna cewa sun dauki matsaya kan wannan al’amari.

  Don haka ina son duniya ta sani cewa gwamnan jihar Zamfara Abdul’azeez Yari bai baiwa Rarara wadannan kudade ba. Don haka wadanda suka fito da wannan magana basu taimakemu ba basu taimaki mawakan APC ba. Domin yanzu sun sa ana zagin gwamna,  yanzu sakamakon faruwar wannan al’amari babu gwamnan da zai yarda ya ganmu, kada shima ace ya bamu miliyan 100.

  GTK; To maye zaka ce kan yunkurin da Abubakar Sani yake yi na kai Rarara kotu kan wannan al’amari?

  Murtala Mamsa; Ai Abubakar Sani  bai san kotu bane, domin idan ya je koyu Karar wa zai yi?. Zai yi Karar Kungiyar mawaKan jam’iyyar ta APC  ne ko  zai  yi Karar gwamna ne ko kuma zai yi Karar Dauda Rarara ne?

  Shi baya cikin Kungiyar nan, shi  yana cikin kwankwasiya ne, a kullum zagin shugaban Kasa Buhari yake yi. Wannan Kungiya kuma ta Buhari ce, saboda  haka baya cikinmu.

  A wannan Kungiya ta mawaKan APC akwai ‘yan PDP da suke son wargaza wannan Kungiya, saboda sun lura Buhari zalla muke yi. Don haka akwai baragwurbi a cikinmu wanda su damuwarsu ya ya za ayi a taba mutumcin shugaban kasa.

  Shi kuma Dauda Rarara ba zai yarda da wannan ba, haka muma ba zamu yarda da wannan ba.

  GTK; To, a nan  wadanne shirye shirye kuke yi, don magance wannan baraka da ta kunno kai a wannan kungiya?

  Murtala Mamsa; Mu bamu da wata baraka a kungiyarmu ta mawakan jam’iyyar APC,     don haka babu wani shiri da muke yi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here