GWAMNA TAMBUWAL YA NADA DINGYADI DA WASU MUTUM BIYAR  S.S.A

0
816
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na Jihar Sakkwato dan takarar shugaban kasa a jam\'iyyar PDP

Rahoton Zubair Sada

GWAMNA Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya amince da nadin alhaji Yusuf Abubakar Dingyadi a matsayin Babban Mai Taimaka Wa Gwamna tare da wasu mutane biyar, wato S.S.A a Turance.

Kafin nadin na Alhaji Yusuf Dingyadi shi ne tsohon Sakataren jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato. Sanarwar mukaman da nadin na cikin wata takardar sanarwa wadda ta sami sanya hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato, Furofesa Bashir Garba.

Sauran mutanen da aka nada S.S.A din kuma suka sami amincewar Gwamna Tambuwal su ne Mustapha Shehu Sokoto tsohon ma’aikacin hukumar kafafaen yada labarai na Jihar sakkwato da Abubakar Ka’oje, tsohon ma’aikacin hukumar gudanarwa ta NTA, sai Kabir Assada, ma’aikacin jarida kuma mai sharhi kan harkokin siyasa sannan ma-dabba’i (mawallafi)  da ke Sakkwato da Muhammad abdullahi Sokoto da kuma Yarima Aminu Mohammed.

Nadin nasu kamr yadda aka bayyana ya fara aiki ne nan take kuma kai-tsaye babu wani tsaiko ko bata wani lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here