Yau Za A Rantsar Da Sababbin Shugabannin Kananan Hukumomi 19 A Kaduna

  0
  659
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
  Kamar yadda wata sanarwa ta fito daga ofishin mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara a kan harkokin yada labarai Mista Samuel Aruwan ta bayyana cewa a yau Laraba ne za a rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomin da aka zaba a kwanan baya a jihar.
  Kamar dai yadda sanarwar ta bayyana cewa da akwai wadansu kananan hukumomi hudu da ba a Rantsar Da kowa ba a matsayin Wanda ya lashe zaben saboda akwai matsalar ko dai ba a kammala zaben ba ko kuma ba a yi zaben ba Sam Sam misali kamar a karamar hukumar Kaura inda ba a yi zaben ba.
  Kamar dai yadda sanarwar ta bayyana za a Nada kantomomin rikon ne a wadannan kananan hukumomi hudu, kuma za a Rantsar Da kantomomin ne tare da Sababbin zababbun da za a Rantsar a Gobe, ranar 26/06/2018
  Kantomomin da za a Nada za su ci gaba da aikin ne har sai an kammala tattaunawar da ake yi da Majalisar dokokin Jihar kamar yadda yake Kunshe a cikin sashi na Bakwai daya cikin Baka 7(1) na dokokin Jihar Kaduna.
  Kananan hukumomin sune Kajuru, chikun, Jaba da Kaura.
  \”Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa a Gobe ne Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i zai Rantsar Da Sababbin Shugabannin Kananan hukumomin da aka zaba a kwanan baya a don haka ne yake taya su murnar yin nasarar lashe zabe da kuma Sabon aikin da za su yi a matakin kananan hukumomi\”.
  \”Jihar Kaduna dai ta kawo tsarin yin zaben kananan hukumomi ne ta amfani da na\’urar zabe domin kara inganta yadda ake gudanar da zaben gaskiya da adalci ta yadda zai samu karbuwa a tsakanin al\’umma\”.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here