Rikicin Jihar Filato: Akalla Mutane 120 Aka Kashe A Sabon Rikicin

0
671
Shin wace siyasa ce ake yi da kashe mutane a Najeriya?
Daga Usman Nasidi Da Mustapha Imrana
\’Yan sanda a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya sun ce akalla mutum 86 ne suka mutu bayan da fada ya barke tsakanin manoma da makiyaya.
Wasu rahotanni sun ce fadan ya barke ne ranar Alhamis bayan da \’yan kabilar Berom suka farma wasu Fulani makiyaya, inda suka kashe biyar daga cikinsu.
Daga nan ne kuma aka ce wani hari na ramuwar gayya ya kai ga kisan wasu karin mutanen.Yankin ya dade ya na fama da rikici tsakanin kabilun da ke rigima kan mallakar filaye.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rikicin, sannan ya sha alwashin hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.
Tun da farko an kashe gwamman mutane a wani rikici mai kama da wannan tsakanin Fulani da mafarauta a kasar Mali.
Kwamishinan \’yan sanda na jihar Undie Adie ya ce binciken da aka gudanar a wasu kauyuka bayan kai harin ya tattabatar da cewa an kashe mutum 86, sannan wasu shida su ka samu rauni.
Ya ce an kona gidaje 50, da baburan hawa 15 da kuma motoci biyu.
Kwamishinan yada labarai na jihar Yakubu Datti ya shaida wa manema labarai cewa dokar hana fitar za ta yi aiki daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe a Riyom, da Barikin Ladi da kuma Jos ta Kudu \”domin hana jama\’a daukar doka a hannunsu da samar da zaman lafiya\”.
Sai dai sabanin bayanin \’yan sanda, Mr Datti ya ce sama da mutum 20 ne suka jikkata, kuma suna samun magani a asibitoci daban daban.
Tare hanya
Rahotanni dai na cewa mutanen yankin da ake rikicin suna tare hanya su na kashe mutanen da \’ba su ji ba, ba su gani ba,\’ wadanda yawancinsu matafiya ne da ke fitowa daga jihohin arewa maso gabas kamar su Bauchi da Gombe da Yobe, zuwa Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here