Sojoji Sun Kama Yan Ta\’adda A Zamfara

0
886
Sojojin Najeriya Babu Wargi
Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
Rundunar sojan Nijeriya Shiyya ta daya da ke da hedikwata a Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar Kama wadansu Yan ta adda tare da wadansu makamai nasu.
Kamar yadda rundunar ta bayyana a wata takardar da suka raba wa manema labarai cewa sun yi nasarar ne a karkashin Shirin da suka yi wa suna IDON RAINI inda suka dirar wa wata maboyar Yan Ta\’addan a kauyen Jambrini a karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara.
An Kuma wannan aikin ne a ranar 23 ga watan Yuli 2018 sojojin sun dai bayar da sanarwar cewa a lokacin wannan aikin kakkabe bata garin an samu nasarar Talata sansanunsu da dama an tarwaza wasu an kuma samu nasarar Kama guda uku wasu kuma sun tsere tare da raunin bindiga a jikinsa.
Kayan da aka samu tare da su sun hadar da bindigar AK 47 da Fito F 99, wayar hannu kirar PTT HH guda daya sai albarusai 111 masu tsawon inci 7.62. bindigogi biyu sai wayar hannu uku da na\’urar cabin waya daya.
Rundunar ta ci gaba da bayani a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai da mataimakin Daraktan hulda da jama\’a na rundunar sojan Nijeriya Kanar Muhammad Dole ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Sun kashi takobin ganin sun magance dukkan ayyukan da irin wadannan batagarin ke aiwatarwa a ko\’ina suka bayyana a cikin takardar ta su cewa an samu nasarar ne sakamakon irin muhimman bayanan da suka samu daga wadansu masu kishin kasa da son ci gaban jama\’a, sai suka bukaci duk wani mai bayanin da zai Kai ga samun nasara da ya hanzarta ba su bayanin da zai Kai ga nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here