Yaron Gida Ya Kashe Maigidansa Wani Soja da Budurwarsa

0
666
Wannan ne yaron gidan da ya aikata mummunar ta\'asa

Daga Usman Nasidi

WANI Yaron gida Raphael Jaja, ya shake budurwar Abubakar har saida ta mutu kafin daga bisani ya yi amfani da wuka ya kashe sojan, sannan ya saka gawar sa cikin wata jaka daya dauka zuwa cikin daji inda ya kone gawar sa.
 

Jaja, dan asalin karamar hukumar Opobo-Nkoro ta jihar Ribas ya ce ya kashe maigidan nasa ne da budurwar sa saboda bai biya shi albashin san a tsawon watanni 15 ba amma ya sayawa budurwar ta sa wayar hannu ta N300,000.

Ya kara da cewa marigayi Abubakar ya yi masa alkawarin zai ke tara masa albashin sa (N15,000 a wata) amma kuma ya saba wannan alkawari day a dauka.

Kafin hukumar ‘yan sanda ta bankado gaskiyar abinda ya faru, rahotanni sun bayyana cewar marigayi Abubakar ne ya kashe budurwar ta sa sannan ya gudu ya buya. Amma daga baya binciken hukumar ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ta, Abba Kyari, ya warware ainihin abinda ya faru.

Hukumar ‘yan sanda ta gano Jaja ne ya aikata laifin bayan gano wayar marigayi Abubakar a hannun wani abokin sa a Fatakwal kafin daga baya su gano inda yak one gawar marigayin da kuma wanda ya sayarwa da motar sa kirar Hyundai a kan naira miliyani N1.9m.

Jaja ya shaidawa manema labarai cewa, ya kashe maigidansa ne saboda ya yi alkawarin bashi miliyan N2.5m bayan ya taimaka masa ya samu wata kwangila ta miliyan N22.8m amma ya gaza cika alkawarin daya dauka kamar yadda ta faru a kan albashin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here