KAFA WURAREN KIWO ZAI KAWO KARSHEN RIKICIN  MAKIYAYA DA MANOMA A NIJERIYA-BAYARI

  0
  915
  Alhaji Sule Bayari

  Isah  Ahmed, Jos 

  A ‘yan kwanakin nan ne gwamnatin Nijeriya ta bada sanarwar cewa ta ware jihohi 10, don yiwa Fulani makiyaya wuraren kiwo irin na zamani guda 94, don magance rikice rikicen Fulani makiyaya da manoma a Nijeriya.  

  Jihohin da za ayi wadannan wuraren kiwo sun hada da Adamawa, Filato,  Benuwai, Nasarawa, Kaduna, Taraba, Ebonyi, Oyo, da kuma Edo.

   A wannan  tattauna da wakilinmu ya yi da shugaban kungiyar cigaban al’ummar Fulani ta Nijeriya, ta Gan Allah Alhaji Sale Bayari kan wannan al’amari. Ya bayyana cewa babu shakka wannan shiri zai kawo karshen rikice rikicen Fulani makiyaya da manoma, a Nijeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK; A yan kwanakin nan gwamnatin Nijeriya ta bada sanarwar cewa zata yiwa Fulani makiyaya wuraren kiwo a jihohin Nijeriya  10,  a matsayinka na daya daga cikin shugaban al’ummar Fulani makiyaya na Nijeriya, mene ne zaka ce kan wannan al’amari?

  Sale Bayari; To, gaskiya mun gode Allah, domin mu dama tura ta riga kai bango kan harkokin makiyaya a Nijeriya. Saboda akwai abubuwa da dama da suka zamarwa al’ummar Fulani makiyaya matsaloli iri iri.

  Kuma tun ba yau ba,   muna ganin gwamnati tana gwada abubuwa da dama, kan matsalolin Fulani makiyaya  amma  abin yaci tura. Saboda na daya an ce ba za a yi kiwo irin na gargajiya ba, wato irin kiwon da aka gada kaka da kakanni, kuma an kawo tsare tsare da dama kan Fulani makiyaya, amma  sun gagara.  Sai ga shi   ‘yan kwanakin nan gwamnatin tarayya ta bada sanarwa fito da wannan shiri, na yiwa manoma wuraren kiwo a jihohi 10 na qasar nan.

  Ina ganin babu shakka za a sami nasara kan wannan shiri musamman ganin cewa gwamnati ta ce zata dauki shekara 10 wajen gudanar da wannan shiri, domin an ce za a fara wannan shiri daga  shekara ta 2018 zuwa shekara ta 2027.

  Babu shakka mu a matsayinmu na shugabannin Fulani makiyaya muna bada goyan baya dari bisa dari, don ganin an sami nasarar wannan shiri.

  GTK; Kamar ta yaya kake ganin al’ummar Fulani makiyaya zasu amfana da wannan shiri?

  Sale Bayari; To kamar yadda gwamnati tayi bayani kan wannan shiri a jaridu da sauran kafofin watsa labarai, babu shakka wannan shiri yana da kyau, kuma al’ummar Fulani makiyaya zasu amfana da wannan shiri ta bangarori da dama.

  Domin na daya duk inda za a zaunar da bafulatani idan ba a tanadar masa da hanyoyin da zai a sami abincin da dabobinsa zasu ci ba, ba zai zauna a wurin ba. Amma matukar aka tanadar masa da abincin da dabbobinsa zasu ci da ruwan sha da makaranta, da asibiti da  kasuwanni da sauran abubuwan kyautata rayuwa to zai zauna a wurin.

  To, kaga  a wannan shiri, gwamnati ta ce zata yi dukkan  wadannan abubuwa kuma zata tallafawa kungiyoyin Fulani makiyaya  za ayi  bankuna da hanyoyin sayen kayayyakin abincin dabbobi da samar  motocin noma don noman abincin dabbobi, kuma za a samar da isashen wurare yadda bafulatani mai shanu 50 ko 100 ko 200 ko 300 za a bashi ya zauna da shanunsa.

  Kuma za a samar da bankunan ajiye maniyyin shanu don yin baye ga shanun makiyaya. Wato za a rika amfani da irin wannan maniyyi kamar yadda ake yi a kasashen da suka cigaba, wato a riqa  yiwa shanunmu baye ta yadda saniya  guda daya zata iya bada ruwan nono kamar yadda shanu  7 namu na gargajiya suke bayarwa. Kuma za a sami  bijimin sa guda daya wanda a cikin shekara 2 zai yi girma kamar wanda ya shekara 7  irin shanunmu na gargajiya.

   Kaga a  za a dauki ‘yayan Fulani makiyaya da suka yi karatun likitancin shanu aiki, a wannan shiri.

  Wato, yadda aka yi tsari a wannan shiri, a hankali bafulatani zai fahimci cewa yawan shanun da yake da su ba shi ne riba ba, yawan ingancin shanun da yake da su, shi ne ribarsa. Domin akwai inda shanu guda 12 za su iya bada nonon da shanu guda 100 irin namu na gargajiya ba  zasu iya bayarwa ba. Akwai inda bijimi sa guda  xaya zai bayar da naman bijimai guda  5 irin namu na gargajiya.

  A takaice a wannan shiri,  za a kawo shanun kasashen waje, a hankali Fulani makiyaya zasu ga cewa maimakon bafulatani makiyaya yana da shanu guda 500, shanu 50 na zamani zasu bayar da duk abubuwan da waxannan shanu  500 zasu bayar. Don haka zasu gano cewa maye zai sanya su rika dibar shanu da yawa, suna wahala ana kashe masu ‘yaya da mata wajen kiwon wadannan shanu.

  Don haka muna ganin wannan shiri na yiwa Fulani wuraren kiwo a kasar nan, yana da kyau kwarai da gaske. Saboda haka mu zamu goyi bayan wannan shiri dari bisa  dari domin muma wadannan rikice rikice sun ishe mu, kuma muma muna son mu cigaba daga inda muke.

  Yawan al’ummar kasar Indiya, ya ninka yawan al’ummar Nijeriya kusan sama da biyar. Kasar China suna da yawan mutane sama da biliyan 1 kasar Amerika tana da yawan mutane sama da 250, maye yasa mutanen wadannan kasashe basa rasa nama, duk da yawan mutanensu?. Har suna fitar da naman zuwa kasashen waje? kamar kasar Indiya tana cikin kasashen da suke fitar da nono zuwa kasashen waje.

  Saboda haka idan aka yi abin da ya kamata a Nijeriya, yawan shanu da ake gani suna ta yawo, motoci suna bugewa ana ta fadace fadace a kansu, ba za a gansu ba sai mutum ya shiga mota kafin yaje wajen da zai gansu.

  GTK; Ganin cewa Fulani makiyaya sun dade suna koke koken cewa gwamnati tayi watsi da su bisa la’akari da wannan shiri, za  a iya cewa wannan gwamnati tayi Fulani makiyaya abin da ba a taba yi masu ba ke nan?

  Sale Bayari; Gaskiya ne, amma  tun kafin a sami ‘yancin kan Nijeriya, turawa sun yiwa Fulani makiyaya tanadi yadda za ayi kiwo batare da shan wahala ba. Domin tun lokacin turawa suka ce a killace huruman kiwo a kasar nan. Har suka bar kasar nan, ba a kammala wannan shiri ba. Amma su marigayi Sarduna suna zuwa aka fitar da tsare tsaren hurumin kiwo sama da  500 a kasar nan.

  Bayan an yi wadannan huruman kiwo, a  zamanin su Sardauna  yanzu huruman kiwon da ake da su a kasar nan basu fi guda 25 ba.

  Saboda haka akwai shirye shirye da aka gwada yi a baya, amma ba a sami nasara ba. Ko a lokacin marigayi tsohon shugaban qasa Umaru Musa ‘Yar aduwa ni ina cikin wadanda aka gayyata karkashin ministan gona na lokacin Sayadi Ruma,  muka zaga arewa gabaki daya muka duba inda aka sanya siminti da yake nuna cewa ga burtalin shanu. Mun zagaya har su Maiduguri, Yobe, Gombe, Bauchi,  Filato, Sakkwato da  dai sauransu.

  Shirye shiryen ana yi ada, amma idan gwamnati ta ce zata yiwa Fulani makiyaya wani abu sai tazo ta fara daga karshe kuma sai azo a bari.

  Amma wannan shiri na yiwa Fulani makiyaya wuraren kiwo da wannan gwamnati ta kuduri aniyar yi, ko don a shawo kan rikice rikicen Fulani makiyaya da manoma in Allah ya yarda za a sami nasara. Domin kowa ya gaji da wannan rikici a qasar nan.

  GTK; To maye zaka ce kan matakin da gwamnatin jihar Ebonye da wasu kabilun jihar Benuwai suka dauka na kin amincewa da wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka?

   Sale Bayari; To, wannan mataki da wadannan mutane suka dauka na kin amincewa da wannan kuduri da gwamnatin tarayya tayi na kafa wuraren kiwo a jihohinsu ya nuna cewa suna yin wannan abu ne da wata manufa ta daban.

  Wato a takaice suna yin wannan abu ne domin su ciwa wasu mutane mutumci. Saboda yanzu ace an abu a jihohi 10, amma  azo a sami wata jiha wato jihar Ebonye da wasu kabilu   a wata jiha su fito su ce basu amince ba,  wannan abin takaici ne.

  Domin kamar  jihar Ebonye gwamnan jihar ne  da kansa  ya zama shugaban kwamitin da mataimakin shugaban kasa da gwamnoni suka   kafa, don fito da shawarwarin kafa wadannan wuraren kiwo. Amma yanzu ace jihar sa ce suka zauna a taron majalisar zattarwar jihar su ce ba su yarda da wannan kuduri ba, wannan abin takaici ne.

  Su kuma jihar Benuwai muna ganin ana amfani da ‘yan siyasa da kungiyoyi ne wajen dakile wannan shiri. Akwai shugabanin kungiyoyin qabilar TV da kabilar Idoma da kabilar Egede da suka fito suka ce basu amince da wannan shiri ba, domin a cewarsu  wai gwamnatin tarayya ne take  son ta kwace masu filaye ne ta baiwa Fulani makiyaya.

  Saboda haka muna son ‘yan Nijeriya da gwamnatin Nijeriya su fahimci cewa ga wadanda basa son a zauna lafiya.

  Amma kaga kamar gwamnan jihar Nasarawa Tanko Almakura shi da yake son a zauna lafiya, ya amince da wannan kuduri, har ya bayar da huruman kiwo  guda 7  a jiharsa  don a aiwatar da wannan shiri.

  Wannan abu da gwamnan jihar Nasarawa ya yi ya nuna cewa shi mai son zaman lafiya ne. Don haka muna rokon sauran gwamnoni su yi koyi da wannan gwamna.

  GTK; To, a karshe wanne kira ko sako ne kake da shi zuwa ga gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohin da aka ware don gudanar da wannan shiri?

  Sale Bayari; Wannan mataki gwamnatin tarayya ta dauka na kafa wadannan wuraren kiwo ga makiyaya a Nijeriya, ya nuna cewa tana da kyakyawar manufa. Don haka sakona a nan shi ne  duk wanda yake son zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya kamata ya rungumi wannan shir,i kuma ya bada goyon baya. Kuma kamar yadda gwamnatin tarayya ta fito ta dauki wannan kuduri muna kira ga dukkan jihohin Nijeriya 36 har babban birnin tarayya Abuja ba wai jihohi 10 kadai ba, su fito su rungumi wannan shiri, wanda muke ganin shi ne zai kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Nijeriya.

  Kuma ina kira ga Fulani makiyaya mu goyi bayan wannan shiri, na kafa wuraren kiwo a Nijeriya saboda mahimmancin da yake tattare da shi.

   

   

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here