Takarar Isa Ashiru Ba Ta A Mutu Ko A Yi Rai Ba Ce – Gayya

  0
  555
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
  DAYA daga cikin \’yan kwamitin yakin neman zaben da suke fafutukar ganin Honarabul Isa Ashiru ya lashe zaben Gwamnan Jihar Kaduna mai zuwa Dan Majalisar wakilai Honarabul Goefree Ali Gayya ya shaida wa manema labarai cewa takarar ba ta a mutu ko ayi rai ba ce.
  Ali Gayya ya bayyana wa manema labarai hakan ne a Kaduna lokacin da kwamitin yada labarai na yakin neman zaben Isa Ashiru suka kai wata ziyara cibiyar \’yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna.
  Gayya, ya ce duk masu yada jita jitar cewa wai shi Isa Ashiru yana kokarin ganin ko ana ha maza ha mata sai ya zama Gwamnan Kaduna ba haka ba ne, yana dai jarabawa ne kawai ya tsaya takara sakamakon irin yadda mutane ke matsa masa lamba sai ya fito domin zama Gwamna.
  \”Isa Ashiru mutum ne mai kyakkyawar alaka da kowane irin mutum, hakika halinsa mai kyau ne kuma yana da kunnen sauraren jama\’a don haka idan an zabe shi lallai ba za a yi da na sanin zaben sa ba\” inji Gayya.
  Ali Gayya wanda Dan majalisa ne na wakilai a halin yanzu daga kudancin Kaduna ya roki \’yan jarida cewa su taimaka domin tallata Isa Ashiru ta yadda za a samu nasarar da kowa ke bukata domin babu wanda zai yi da na sani idan suka lashe zaben Jihar.
  Ya kuma bayar da tabbacin cewa dukkan alkalumma sun fito cewa su za su lashe wannan zabe a shekarar 2019 mai zuwa in Allah ya yarda.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here