Ya Kafa Kwamitin Binciken Kashe Jami’ansa 7 A Abuja

0
521
I G Na \'Yan Sandan Najeriya
Rabo Haladu Daga Kaduna
BIYO bayan kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa ‘yan sanda bakwai cikin Birnin
Abuja, babban sifeton rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris, ya kafa
kwamitin bincike a karkashin shugabancin Kwamishanan ‘yan sanda Bala Ciroma
Alhaji Ibrahim K. Idris, shugaban ‘yan sandan Nigeria ya kafa kwamitin da zai binciki kisan ‘yan sanda bakwai da wasu ‘yan bindiga suka yi a Abuja.
Ya umurci kwararrun ‘yan sandan da za su gudanar da binciken a karkashin jagorancin Kwamishanan ‘yan sanda Bala Ciroma da su gudanar da gaggarumin binciken domin gano ‘yan bindigan da suka bindige ‘yan sanda bakwai a cikin Birnin Abuja a kwanakin baya.
Wata sanarwa da hedkwatar ‘yan sandan ta fitar na nuna cewar wadannan ‘yan sanda
masu bincike an umurce su da su binciko manufar ‘yan bindigan da suka yi aika aikar, kana su bayyana yadda za a magance sake aukuwar hakan nan gaba.
Bala Ibrahim mai magana da yawun shugaban ‘yan sandan yana mai cewa babban sifetonsu baya daukan irin binciken da wasa. Duk lokacin da wani abu ya faru yana cewa a gaggauta bincike a yi bincike mai zurfi da zummar shawo kan lamarin a kuma magance shi ta hanyar kamo masu laifin a gurfanar da su gaban shari’a.
Bala Ibrahim ya ce shugaban ‘yan sandan ya gayawa masu binciken su gudanar ta yadda ‘yan Nijeriya za su gamsu.
Masana tsaro irin su Malam Kabiru Adamu ya yi maraba lale da daukan matakin. To amma sai dai ya ce matsalar ita ce a Nijeriya a kan yi saurin kafa kwamitin bincike amma da zarar
sun kammala aikinsu sai a ji shiru kamar an shuka dusa, ba a daukar wani mataki ko yin amfani da sakamakon binciken.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here