MAKARANTAR AZMARATU TA SHIRYA BIKIN TUNAWA DA RANAR AL’ADU TA DUNIYA

0
705
Daliban makarantar Azmaratu a wajen taron

Isah Ahmed, Jos

MAKARANTAR koyar da ilmin addinin Musulunci da ilmin boko ta Azmaratu da ke garin Narabi, a karamar hukumar Toro da ke jihar Bauci ta shirya bikin tunawa da ranar al’adu ta duniya, a karshen makon da ya gabata.

Da yake jawabi a wajen taro wanda ya gina makarantar, Sheikh  Mu’azu Umar Na’annabi ya bayyana cewa babu shakka gina irin wadannan makarantu yana da matukar alhairai masu tarin yawa. Don haka ya yi kira ga masu hannu da shuni su rika kokari suna gina irin wadannan makarantu.

Ya yi  kira ga malamai da daliban wannan makaranta su sanya Allah a cikin ilmin da suke nema. Domin ba a samun albarkar ilmi, sai an sanya tsoran Allah a cikin neman ilmin da ake yi.

Shi ma a nasa jawabin shugaban makarantar Malam Muhammad Saminu Abbas ya bayyana cewa sun shirya wannan biki ne  don kawo hadin kai tsakanin al’ummomin da suke zaune a wannan yanki.

Ya ce babban burinsu ga wannan makaranta shi ne samar da ingantatcen ilmi ga al’ummar yankin. Ya ce suna son duk dalibin da ya yi karatu a wannan makaranta kafin ya kammala,  ya iya harsunan Larabci da Turanci da kuma haddace Alkura’ani mai girma.

A wajen wannan taro dai, an gabatar da shigar suturun kayayyakin sawa na gargajiya na kabilu daban daban da wakoki da raye raye da abinci na kabilu daban daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here