Shugaban  karamar hukumar Kudan Zai Magance Matsalar Tsaro Da Kawo Ci Gaban Al\’ummar Yankin Sa

0
646
Gwamna Malam Nasir El-Ruffa\'i na Jihar Kaduna

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABAN Karamar Hukumar Kudan  Honarabul Shu’aibu Jaja ya bayyana cewa gwamnatinsa zata mayar da hankali a kan harkokin tsaro da cigaban al\’ummar yankin domin koyi da kokarin gwamnan malam Nasiru El-Rufa’I dayakeyi a  fadin jihar baki daya.

Shugaban ya bayyana cewa samar da tsaro da cigaban al\’umma shi ne abu mafi muhimmanci ga ci gaban kasa.

Yace  hakanne  ya sanya suka dukufa wajen tabbatar da cewa sun magance matsalar yara masu zaman banza a duk  fadin karamar hukumar ta Kudan.

Honarabul Shu’aibu, Jaja ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa inda yace majalisar karamar hukumarsa zata tabbatar da cewa ta Kawo abubuwan ci gaban al’umma ta bangarori daban-daban.

Jaja ya kuma Bayyana gamsuwarsa dangane da irin matakan da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i, yake dauka wajen magance matsalar yara ‘yan sara suka a fadin jihar yana Mai cewa; suma a matakan Kananan Hukumomi zasu tabbatar da cewa sunyi koyi da irin matakan da Gwamnan ya dauka domin ciyar da kaduna gaba.

Shugaban Ya ci gaba da cewa ” yanzu haka mun Fara gudanar da ziyara zuwa ga jami’an ‘yan sanda da hakimai da ke cikin wannan karamar hukumar domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da allurar rigakafi yace  Ina Mai tabbatar da cewa zamu bayar da tamu gudummawar wajen tabbatar da an samar da tsaro a fadin wannan karamar hukumar ” inji shi.

Akan hakan shugaban ya bukaci daukacin al’ummar karamar hukumar da su basu goyon Bayan da ya kamata domin ganin sun sauke nauyin da al’ummar karamar hukumar suka basu.

Haka kuma ya bukace su da su zama masu bin doka da samar da hanyoyin zaman lafiya a duk inda suke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here