An Nada Sabon Kwamishinan Yan Sandan Babban Birnin Tarayya

0
687
Daga Usman Nasidi

A ranar Alhamis 19 ga watan Yuli, sabon kwamishinan Bala Ciroma, ya karbi ragamar wannan babban mukami ne a shelkwatar hukumar yayin bikin karbar kujerar daga hannun wanda ya ci gajiyar sa, Sadiq Bello.

Bala Ciroma ya yi karatun digiri din sa na farko a jami\’ar Maiduguri a fannin nazarin yanayi da albarkatun kasa. Ya fara aikin damarar ne a watan Maris na shekarar 1990 a matakin ASP (Assistant Superintendent of Police).

A sakamakon yanayi irin na aikin \’yan sanda, Bala Ciroma ya rike mukamai daban-daban tare da yawon karo karatu a nan gida Najeriya da kuma kasashen ketare inda ya yi karatu a jami\’ar Birnin Hong Kong na kasar Sin a fannin nazarin cin hanci da rashawa.

Majiyarmu ta samu labarin cewa, sabon kwamshinan \’yan sandan ya rike mukamai daban-daban cikin matakai da dama a hukumar ta \’yan sanda musamman a garuruwan Kano, Neja, da Abuja.

Mista Ciroma yayin bayar da tabbacin jajircewar sa bisa aiki, ya nemi hadin kai na al\’umma, kungiyoyi da sauran hukumomin tsaro wajen cimma manufa ta yakar duk wani nau\’in ta\’ddanci cikin babban birnin kasar da kewaye.

Kazalika sabon kwamishinan ya tunatar da dukkanin masu ruwa da tsaki wajen shigar da rahotanni ga hukumar da za su taimaka wajen fatattako miyagun mutane daga mobayar su ta hanyar kiran wannan lambobin kamar haka; 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here