Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Mayar Da Masarautar Zuru, Argungun, Yawuri, Saniyar Ware __Sani Haliru Maiwa

0
592
Rabo Haladu Daga  Kaduna
WATA kungiyar hadin kan \’yan masarautun Zuru, da Argungu da Yawuri ta koka da
yadda aka mayar da masarautunsu saniyar ware a yayin da masarautarGwandu ta mamaye komai.
A yayin wani gangamin da kungiyar ta kira da zummar hadin kan masarautun uku,
wadanda take ganin an mayar saniyar ware, shugabanta Sani Halliru Maiwa, ya ce burinsu shine a zabi gwamna daga cikin masarautunsu a zaben da za a yi a shekarar 2019.
\”Saboda idan ba gwamna muka yi ba, duk abin da muke bukata ba za mu samu ba,\” inji Maiwa. Ya bayyana abin da suke ganin a matsayin rashin adalci, yadda duk manyan mukamai kama daga minista, da gwamna, da kuma jakadu duk sun fito ne daga masarautar Gwandu.
Kodayake akwai wasu mukaman da wadannan yankunan ke rike da su kamar na mataimakin gwamnan jihar, da sakataren gwamnatin jihar da sauransu da ake ganin an kwatanta,
Maiwa ya ce wadannan matsayin jeka- na-yi-ka ne musamman mukamin
mataimakin gwamna.
Sannan Maiwa ya musanta cewa wani dan siyasa ne ya sa su fitowa gangamin da suka yi, domin share masa fage guda uku da suka hada da Gwandu, da Zuru, da Argungu, da kuma Yawuri. Gwandu tana da kananan hukumomim 10 daga cikin 21 da jihar ke da su, yayin da sauran yankunan uku ke da 11.
\”Argungu, da Yawuri, da Zuru su kadai ba su iya kawo canji idan ba su hada da Gwandu ba,\” inji Shugaban ma\’aikata na fadar gwamnatin jihar Kebbi, Suleman Muhammad Argungu, wanda ya taba jagorantar wani yunkuri makamancin haka a can baya. A
cewarsa saboda dukkanin masarautun guda hudu na da hakki.
Ya ce watakila wadanda suka yi gangamin sun yi ne bisa rashin sani, ko son zuciya, kuma turbarsu ba za ta kai su ga cin gaci ba. \”Domin idan aka fidda wani bangare ba a sa wani bangare ba, to za a ga kamar ana yakar wasu ne,\” inji shi.
To ko me ya banbanta wannan gwagwarmayar da wancan da shi Suleiman Muhammad suka yi a baya?
Ya bayyana abinda ya ke ganin a matsayin kuskure ko son zuciya inda kamar ake son ware wasu. A cewarsa, kamata ya yi a jawo kowa a cikin harkar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here