Sarkin Ilori Ya Bai Wa Bukola Saraki Mamaki Da Abin Al\’ajabi A Fadarsa

0
577
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki

Daga Usman Nasidi

MAI martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari ya baiwa Shugaban majalisar dattijan Najeriya Dakta Bukola Saraki mamaki lokacin da ya nadashi sarautar Wazirin masarautar Ilori ba tare da sanin shi ba.

Sarkin dai kamar yadda muka samu ya nada shi sarautar ne lokacin da ya kai masa ziyara a fadar sa a cigaba da rangadin godiya ga Allah da yake yi biyo bayan nasarar da ya samu a kotun koli akan shari\’ar sa da yayi da kotun da\’ar ma\’aikata a kwanan baya.

Majiyarmu ta samu cewa sarautar ta Wazilin Ilori dama a hannun mahaifin sa Dakta olusola Saraki take kafin rasuwar sa.

Wani babban dan siyasa kuma jigo a jam\’iyyar PDP a arewacin Najeriya dake zaman shugaban jam\’iyyar a jihar Adamawa, Tahir Shehu ya bayyana mai neman tikitin takarar shugabancin kasa a jam\’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da cewa shine kadai zai iya kayar da Buhari a zaben 2019.

Kamar dai yadda Tahir din ya bayyana, gogewa da kuma karbuwar dan takarar a dukkanin fadin kasar sune manyan abubuwan da yakama jama\’a su kalla.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here