Wata Sabuwa: Mahaifina Na Nan Da ransa – Inji Dan Marigayi Gaddafi

0
565
BABBAN dan marigayi shugaban kasar Libiya Mu\’ammar Gaddafi watau Saiful Islam a wata fira da manema labarai da ya yi karin haske game da mutuwar mahaifinsa kimanin shekaru da dama da suka gabata.

Majiyarmu dai da dama daga kasar Ivory Coast ta ruwaito cewa Saiful Islam ya ce wata mata mai suna Zayraf Aya da ke a kauyen su Marigayi Gaddafin ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar yana da rai kuma tana ganinsa a kai-a kai kuma yanzu haka yana jinya amma da zaran ya samu lafiya zai koma kasarsa don ceto al\’umarsa.

Hakazalika wasu rahotanni na bayyana cewa haka ma dai matar mai shekaru 35 a duniya ta yi ikirarin cewa Mu\’ammar Gaddafi din shi ne mahaifin \’yarta kuma ta ce ya rasa kafarsa daya sakamakon hare-haren bama-baman da aka kai masa, a lokacin da aka nemi hambarar da mulkinsa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa biyo bayan wata guguwar sauyi da ta tashi a yankin gabas ta tsakaiya an ruwaito cewa \’yan tawayen kasar Libiya sun hambarar da gwamnatin Mu\’ammar Gaddafi a shekarar 2011.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here