APC Ta Fitar Da Dan Takararta Na Zaben Cike Gurbin Kujerar Sanatan Katsina Ta Arewa

0
634
Rahoton Mustapha Imrana
SAKAMAKON irin yadda Dan Majalisar wakilai ta Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kankiya, Kusada da Ingawa wato Alhaji Ahmad Babba Kaita a karkashin Jam\’iyyar APC halin yanzu ya lashe zaben fitar da Gwani domin takarar zama sanata mai wakiltar mazabar yankin Daura da ake kira Katsina da Arewa.
Shi dai zaben za a yi shi ne sakamakon rasuwar Sanata Mustapha Bukar Madawakin Daura da yake wakiltar yankin domin a cike gurbin da ya bari na wakilcin mutanen yankin.
\"\"A zaben fitar da Gwani da aka yi a karkashin APC Wanda ya samu halartar masu ruwa da tsakin  jam\’iyyar an sanar a gaban jama\’a cewa Honarabul Alhaji Ahmad Babba Kaita ne ya lashe zaben da yawan kuri\’u 1,723 daga cikin kuri\’u dubu 3,879 da aka tantance masu jefa kuri\’a.

Kamar yadda hukumar zabe ta kasa ta sanar a kwanan baya cewa za ta gudanar da zaben cike gurbin ne a ranar 1 ga watan Ogusta mai zuwa biyo bayan rasuwar Sanata Mustapha Bukar da ke wakiltar yankin. An dai Fara zaben fitar da Gwani ne a ranar Daren  Laraba kuma an kammala da karfe 1:50 na ranar Jama\’a.

Wanda ya sanar da sakamakon jami\’in zabe Patrick Obahiagbon, a ranar Juma\’a ya ce Ahmad Babba Kaita ya samu kuri\’u 1,723 yayin da Nasiru Sani Zangon Daura ya samu kuri\’u dubu 1,474 daidai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here