\’Yan Bindiga Na Tayar Da Garuruwa A Zamfara

0
561
Sojojin Najeriya Babu Wargi
Rabo  Haladu Daga Kaduna
ADADIN yawan mutanen da ke gudun hijira na ci gaba da karuwa a jihar Zamfara sakamakon hare-haren \’yan bindiga da suka addabi kauyukan jihar.
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce akalla mutum dubu goma sha takwas suka kaurace wa
muhallansu sakamakon sabbin hare-haren \’yan bindiga.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya shaida wa manema labarai cewa kauyuka kusan 20 ne jama\’arsu suka yi kaura a karamar hukumar Zurmi kadai.
Ya ce mutanen sun watse a kauyukan na mazabu uku wato Mashema da Birane da kuma
kwashabawa a karamar hukumar mulki ta Zurmi.
Mutanen kauyukan suna yin kaura ne zuwa cikin garin Zurmi, wasunsu suna asibitin MDG, wasu kuma mallya, mutane da dama aka kashe tare da kone gidaje a hare-haren na \’yan bindiga. Kuma mutane na gudun hijira ne don guje wa hare-haren da kuma garkuwa da su.
Al\’amarin, a cewar wasu mazauna kauyukan jihar ya kai har da rana tsaka \’yan bindiga na iya zuwa su sungumi mutum zuwa daji har sai an biya kudin fansa.
An dai kashe daruruwan mutane a Zamfara a tsawon shekara shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar
Jama\’ar yankin na sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdul\’aziz Yari da gazawa wajen shawo kan matsalar.
Sai dai gwamnatin ta nace cewa tana yin iya kokarinta domin ganin ta kawo karshen lamarin, wanda ya fara haurawa zuwa makwabtan jihohi irinsu Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here