Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ramalan Yero Zai Tsaya Takara

  0
  622

   

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  TSOHON Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Dakta Muktar Ramalan Yero Ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar kujerar Gwamna Jihar karkashin Jam\’iyyar PDP.

  Muktar Ramalan Yero Ya dai bayyana wannan Aniya tasa ne a lokacin da ya Kai ziyara ofishin jam\’iyyar tare da magoya bayansa.

  Ya dai shaidawa shugabanni tare da magoya bayan PDP cewa kowa yana da ikon neman wannan kujera ko duk wata takara amma fa dole a Sani Yan takara kala uku ne.
  Na farko akwai \”Wanda yazo takara domin Allah, na biyu, akwai masu takara domin neman suna, sai na uku, kuma sune Yan a bata don haka a Lura sosai\”.

  Ya Kuma kara ankarar da jam\’iyyar cewa dole fa a yi wa jama\’a abin da suke so, domin a samu abin da ake so daga wurin jama\’a.

  Ya ci gaba da cewa \” Alhaji Muhammadu Namadi Sambo ya bashi kwamishinan kudi ya kuma gode, Marigayi Patrick Ibrahim Yakowa ya bashi Mataimakin Gwamna Shima ya gode Masa Kwarai sai Kuma mai kowa mai komai Allah Madaukakin Sarki da ya bashi Gwamnan Jihar Kaduna baki daya duka babu komai sai Hamdala ga Allah\”.

  Ya kara da cewa tsawon shekaru biyu da ya yi a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna ya aiwatar da dimbin ayyukan ci gaban Jihar tare da al\’ummarta baki daya don haka a duba wanda ya yi aka gani da wanda ke son zai yi ne domin tantancewa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here