CIN AMANAR WAMAKKO CE SILAR CANZA SHEKAR TAMBUWAL DAGA JAM’IYYAR APC

  0
  1021
  Mulkin Gwamna Aminu Tambuwal na tallafa wa rayukan al\'umma baki daya

  DAGA ZUBAIR A.SADA

  RUGUNTSIMIN da ke ta faruwa a fadin kasar nan na canza sheka a jam’iyyun siyasa, alamu na ta kara fitowa daga wurare daban-daban cewa, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya shiyta tsaf domin ya jefar da mangwaro domin kuda ya daina binsa, wato ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP. Hakan babu mamaki a wajen masu fashin bakin siyasa, amma a wurin al’umma baki daya wadanda har ya zuwa yau din nan suna cikin fargaba kan fitar da daya kuma fitaccen Gwamna daga jam’iyya mai mulki, wajibi ne a fito fili a bayyana abubuwan da suka baci tare da ita APC kila yin hakan zai warware zare da abawa da ake famar yi kan canza shekar ta Tambuwal ga al’umma.

  Wata kafa ta ‘online’ ta fitar da rahoton cewa shirin da Gwamna Tambuwal ya kirkira na kiwon dabbobi (shanu) a Sakkwato shi ne ya sanya gwamnatin tarayya fushi da shi saboda ita ma tana yunkurin ta kafa irin wannan shirin, wai shi ne ya sanya shi canza sheka, wannan sam babu kashin gaskiya a cikinsa.

  A shekarar 2015 babu wani tababa, a fili yake cewa, Wamakko yana da kwarjini a sjiyasar Sakkwato, sannan ayyukansa ma sun tallafa wa Aminu Waziri Tambuwal ya sami nasarar kayar da Sanata Abdallah Wali na PDP ya zama Gwamnan jihar Sakkwato tare da hakikanin gaskiyar cewa, an aminta da irin kokarinsa na kasancewa jajirtaccen mamba na majalisar wakilai da hangen nesansa ga kasar nan da rashin nuna kyamarsa ga sauran kabilu da ficensa a wajen jama’a na jam’iyya da jama’ar addini da na kabilu, duka wadannan ne suka kasance jarinsa inda ya zama mafi soyuwa da karbuwa a zaben kujerar Gwamna a shekarar 2015.

  A matsayinsa na mutum mai dimbin hakuri a fagen siyasa da sauraren shawarwari, Tambuwal ya fahimci amfanin yadda za a yi aiki tare da jama’ar siyasar Wamakko da suka yi zagi da makarbiya wajen bibiyar zabensa domin ya kawo zaman lafiya a al’ummar APC ta jihar nan baki daya. Tambuwal ya yi imani da tattaunawa tsakani, domin a fito da shawarwari, a kuma yi aiki tare domin amfanin jama’ar jihar nan kwata. To, ta hakan ne ake samar da bangaren mulki mai tafiya a ginke da tunani mai kyau.

  Domin ya nuna shi mai magana daya ne, kafin zabe Tambuwal ya kyale Wamakko ya zabar masa mataimakin gwamna na yanzu Ahmed Aliyu, kuma bayan shi ma Wamakko ya sanya masa kwamishinoni da dama a manya-manyan ma’aikatu. Za ka sha mamaki idan aka ce maka cewa, ya bar Wamakko ya zaba masa kusan dukan Ciyamomin mulki na jihar. Aminu Waziri ko shakka babu amintacce ne kuma shugaban kwarai. Domin ya girmama tsohon Gwamna Wamakko ya bar shi kusan dukkan nade-naden mukaman gwamnati na ko ina sai har ya amince ya rattaba hannu a kansu kuma ya kwashi kaso mafi tsoka ga mukaman ga jama’arsa’

  Haka domin ya lalata matsayin tattalin arzikin jihar, ya bar ‘Baitul malin’ gwamnati babu ko sisi a cikinta sai dai dimbin bashi, wanda har yau bai ce uffan bag a kowa kan hakan, ya yi shiru kan almundahana da watsi da mulkin na baya wato gwamnatin Wamakko ta yi da dukiyar jihar, ya bar wa cikinsa, shi kuwa Wamakko sai tinkaho yake yi na ganin ai shi ne maigidan dukan ‘yan siyasar jihar ta Sakkwato.

  Abin da ya karya wa Rakumi kashin baya shi ne, yawa-yawan ayyukan da Wamakko ya yi watsi da su wadanda ba a kammala ba, aka ci gadonsu inji wata majiyarmu mai tushe, ta ce yawancin ayyukan nan an rigaya an biya kudadensu amma an ki a aiwatar da su, kuma wasu an fara an ki ci gaba an yi watsi da aikin, Gwamna Tambuwal ya ci gaba da yin su har ya kammala su duka, ya biya basussukan da aka bari, sannan abin mamaki shi ne yawa-yawan ‘yan kwangilar duka jama’ar Wamakko ne masu goyon bayansa, wannan ya kai Tambuwal ba zai iya fito da sababbin ayyuka na kashin kansa ba, kenan an dora wa sabon mulkin nauyin matsalar rashin kudaden yin ayyuka.

  Rashin gamsuwarsa kan wannan al’amari ya sanya kodayaushe Tambuwal yana tuntubar Wamakko a kan kowane lamari kafin ya dauki mataki. Da yake shi dan siyasa ne mai biyayya, yana gaida Sanatan kamar yadda al’adar gaisuwa a kasar Hausa take, yana kiransa yayansa kuma shugabansa a siyasance. Shi kansa Wamakko a gidansa ya taba fada wa taron jama’a cewa, ‘’Tambuwal yana nan a matsayinsa na mai girmama ni, kuma tare da yi mani biyayya matuka, kai ko da dana na cikina ba zai yi mani abin day a fi haka ba’’. Kai hart a kai ma ana cewa, Tambuwal yana ci gaba da biyan abubuwan da ake kashewa a gidan Wamakko a banki duk da kasancewa yana da mataki na Sanata mai ci a tarayyar Najeriya. To, akwai biyayyar da ta fi haka?

  KULLE-KULLEN SIYASA

  Tarihi ya nuna cewa, jam’iyyun siyasa a Najeriya suna zagayawa ne a tsakankanin daidaikun mutane ko iyayen siyasa wadanda suke daukar kawunansu cewa su suka fi kowa iya juya akalar siyasa a inda suke. Shi Tambuwal ya yi imani cikakke a kan shugabannin siyasarsa kuma yana biye da ajendarsu sau da kafa atsakaninsa da Allah.

  Da yake baya da masaniyar komai na cewa, Wamakko yana son ya yi watsi da shi daga kujerar mulkin na Gwamnan jihar, majiyarmu ta ce Sanatan yana son ya sanya dan takararsa Faruk Yabo tsohon kwamishinan kudi da kananan hukumomi ko Ahmed Aliyu mataimakin Gwamna na yanzu. Daga nan aka fara kulle-kullen da yarfen siyasa.

  Abin mamaki shi ne Gwamna Tambuwal da Sanata suna tare a fagen al’amuran da suka shafi al’ummar da suke jihar Sakkwato, inda za ka gane hakan shi ne dukansu sun yi magana a kan yadda gwamnatin tarayya ta yi biris da batun nan na daukar ayyuka, da ayyukan da tarayyar Najeriya take yi da sauransu. Gwamnan ya roki gwamnatin tarayya kan batun Dam na Gwaranyo wanda ya kafe ya sanya rayukan al’umma sama da miliyan 4 cikin rashin wadataccen ruwa, amma gwamnati shiru kake ji, wai malam ya ci shirwa. Gwamnonin yankin Dam na Gwaranyo su 2 suka yanke shawarar canza sheka zuwa PDP, wannan shi ne dalilin rashin jituwarsu da gwamnatin Muhammadu Buhari.

  Cikin sa’a aminan Gwamna Tambuwal da suke a fadar shugaban kasa sun sanar da shi abubuwan da suke wakana na yawa-yawan taron da Wamakko yake yi da yaran siyasar shugaba Buhari inda yake cin naman Tambuwal, yana yi masa batunci tare da kazafi daban-daban na karya. Kai har ta kai ma Wamakko ya ce shi daya zai kawo wa APC jihar a zaben shugaban kasa na 2019, amma da sharadin idan an taimake shi an yi watsakali da Tambuwal aka ajiye shi gefe daya. Tambuwal da yake shi ba mai son hayaniya ba ne, ya yi duk wadda zai yi domin ya gana da shugaban kasa domin ya wanke kansa daga sharrukan da aka ce ya yi, wato dai ya fitar da tsakuwa daga gari, amma al’amarin ya ci tura, Wamakko ya shige gabansa domin neman girma shi kadai kawai.

  Kwatsam sai aka wayi gari jihar da ked a zaman lafiya, ‘yan bindiga sun kutsa kai sun kai samame suka kasha mutum 32 a karamar hukumar Rabah a kwanakin baya. Tambuwal ya yi bakin cikin wannan lamari inda ya danganta hakan ga gazawar shugabanci a can sama na kasa baki daya ya fadi cewa,’’yadda ake ta kashe rayukan bayin Allah wadanda ba su ji ba ba su gani ba ya kawo wa daukacin kasar nan rashin tsaro. Ba abin da ‘yan Najeriya suka zaba ba kenan a shekarar 2015’’, inji Tambuwal

  To wadannan kalamai na Gwamna Tambuwal su ne abin da Wamakko ya yi amfani da su  domin ya kara rura wutar fitina tsakanin Tambuwal da mulkin shugaba Muhammadu Buhari. Wasu ‘yan awoyi kadan bayan jawabin gwamna Tambuwal da ya so a karfafa shugabannin tsaron kasar nan, aka kai wa Tambuwal wani hari tare da tambayoyin kure, daga ofishin manema labarai suna kalubalantarsa na cewarsa shugaban kasa GCFR ne ke da alhakin kashe-kashe na Rabah, don haka wannan ya sanya aka nuna cewa, Tambuwal shi ne makiyi na daya, ya shiga bakin littafin fadar shugaban kasa da ke ‘Aso Rock’, wannan duk da iza wutar da ‘yan kungiyar Wamakko da suka shuka zarginsu a kan jawabin Gwamna Aminu Tambuwal din.

  MATSAYA

  Al’amarin adawar da batunci da rashin gaskiya a fili ya bai wa jama’a da yawa-yawa ‘yan asalin jihar Sakkwato al’ajabi cewa, Sanata Wamakko zai ha’inci tare da yaudara da cin amanar Gwamna Tambuwal wanda yake tamkar yaron day a Haifa a cikin shekaru 3 da suka wuce yana ofis, Aminu Tambuwal yana ta biyayya yana biye da ra’ayin shugabanninsa na siyasa da dadi babu dadi a gare shi da ma dimbin magoya bayansa.

  Amma ga duk mutumin da ya san wane ne Wamakko da hargowar siyasarsa, cin amanar tambuwal ba za ta zo masa da mamaki ba, domin Wamakko ya taba yi wa shugabansa Bafarawa cin dunduniya. Tarihi na nan a rubuce na cewa, yadda Wamakko ya yi watsi da shugaba Muhammadu Buhari daga karshe inda ya bi tawagar PDP ta Olusegun Obasanjo bayan ya karbi tikitin takararsa na Gwamna a tutar jam’iyyar APC, inda ya babbake kenan ya hana kowa tsayawa takara dalilin rashin lokaci.

  Damalmalewar al’amuran siyasar da babakeren Wamakko da yake yi wa Gwamna Tambuwal, magoya bayansa suka yunkuro tare da mutanen alheri na Jihar Sakkwato suka karfafa masa gwiwa da goyon bayansu dari bisa dari ga dukan inda ya dosa a siyasarsa, suka ce wani hani ga Allah baiwa ne, suna tare da shi. Lokaci ya yi da zai dauki ragamar tafiyar da yake yi ba tare da bibiyar Sanata Wamakko ba, zai iya canza sheka, domin komawa wata jam’iyya, su a Sakkwato mutum nagari irin Tambuwal suke bukata ba ‘yan hayaniya ba. ‘’Mutum daya kamar Tambuwal kwakkwara ya fi masu mutane miliyoyi yuyuyu’’.

  Haka kuwa aka yi, ko ni mai rubutun nan shaida ne, domin a yau Laraba 1 ga watan Agusta ina fadar gwamnatin jihar Sakkwato inda aka yi taro har taro na masu ruwa da tsaki da ‘yan jama’ar da suka ji sanarwar amma fa dubban jama’a ne inda aka ji bayanai tare da amincewar jama’a Rt.Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya canza sheka daga APC zuwa PDP. Hausawa na cewa, ‘’ Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta’’. Tambuwal Larabarsa ya gane Juma’arsa mai kyau ce a wurin Allah SWT.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here