An Zargi \’Ya\’yan APC Da Cin Hancin Dubu 750 A Dakatar Da Shehu Sani

  0
  607
  Ciyama na NUJ, tare da Kwamared Ado da Kwamared Bashir
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
  WADANSU \’ya\’yan kungiyar kokarin tabbatar da samun ci gaba a jam\’iyyar APC daga jihar Kaduna sun yi kira da babbar murya inda suka bukaci uwar jam\’iyyar ta kasa da su sanya baki a kan irin yadda wadansu ke kokarin taka kundin tsarin mulkin APC sakamakon son zuciya.
  Wannan kiran daga bakin Kwamared Bashir Yakubu, mai fafutukar ganin APC ta ci gaba da rike mutuncinta da kuma nasarorin da aka santa da su a fadin Jihar Kaduna,kasa tare da duniya baki daya.
  Kwamared Bashir Yakubu, ya ci gaba da cewa hakika \’yan a fasa kowa ya rasa na neman yi wa jam\’iyyar APC illar da za ta haifar da wani abu sabanin abin da aka saka a gaba na ci gaban kasa tare da al\’ummarta gaba.
  Bashir Yakubu, ya shaida wa manema labarai a Kaduna cewa a batun gaskiya jama\’a da dama sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da cewa wai an dakatar da sanata Shehu Sani daga cikin jam\’iyya, har wasu da dama suna yin suka game da lamarin.
  \”Bayan mun gudanar da bincike a kan irin yadda batun dakatarwar ya kasance mun gano cewa tabbas kudi sun canza hannu domin shugabannin mazaba su aiwatar da batun dakatar da Sanatan daga jam\’iyyar\”.inji kwamared Bashir.
  Da yake karin haske a kan lamarin Kwamared Ado Muhammad Sani ya tabbatar wa da manema labarai a cibiyar \’yan jarida cewa da akwai \”wani daga cikin mukarraban gwamnatin da Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i, ke wa jagoranci suna da tabbacin ya raba wa shugabannin APC  kudi domin su sa hannu cewa sun dakatar da Sanata Shehu Sani daga cikin jam\’iyyar APC har sai illa-masha Allah\”.Inji kwamared Ado.
  Bashir Yakubu ya kuma shaida cewa nan gaba kadan za su kawo wa manema labarai wadanda aka ba kudin domin kowa ya ji daga bakinsu, wanda hakan ya sa tabbatar da shaida.
  Ya kuma ce a cikin wata takardar da ya rabawa manema labarai cewa sakamakon rashin bin dokokin da suke a cikin kundin tsarin mulkin jam\’iyya, ya sa tsohon shugaban APC na kasa Cif John Oyegun ya ce su a matsayinsu na shugabanni na kasa baki daya sun haramta wannan batu baki daya, don haka babu wata magana mai kama da hakan sam-sam.
  Kwamared Bashir Yakubu tare da tawagar da suka zo cibiyar manema labaran da su sun raba wa daukacin \’yan jaridar da ke wurin kundin tsarin mulkin jam\’iyyar APC domin kowa ya rika samu abin dogaro a duk lokacin da wani abu ya taso da ya shafi APC.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here