Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

0
477

 

Daga Usman Nasidi

MATAIMAKIN gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya yi murabus bayan an shafe watanni ana takun saka tsakaninsa da Gwamnansa Dokta Abdullahi Ganduje.

Mataimakin gwamnan ya sanar da murabus din nasa ne a wata wasika da ya mika wa Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Ganduje.

A cikin wasikar, ya ce ya so ya ci gaba da rike mukamin mataimakin gwamna har zuwa karshen wa\’adin mulkin da aka zabe su, amma ya sauka ne saboda matsalolin da suka dabaibaye dangantakarsa da gwamnan jihar.

\”Ina sanar da kai cewa na yanke shawarar sauka daga mukamin mataimakin Gwamnan jihar Kano daga ranar Asabar 4 ga watan Agusta, 2018.

A cikin wasikar, ya kara da cewa, \”Idan baka manta ba mai girma Gwamna, na sha jan hankalinka ga wasu batutuwa da ka iya tada husumar da muke fuskanta a yau, amma kokarin nawa bai yi nasara ba.\”

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.
A wata hira da ya yi da manema labarai, kwamishinan ya ce mataimakin gwamnan ya mika takardar barin aiki a fadar gwamnatin jihar Kano.

\”Na bincika, kuma na tabbatar da cewa ya gabatar da wannan takarda a gidan gwamnatin, kuma mun duba takardar da abin da ta kunsa.\”

Kwamishinan ya kara da cewa, \”Abin da yake nunawa shi ne cewa ya bar aiki a matsayinsa na mataimakin gwamnan jihar Kano.\”

Da aka tambaye shi ko Gwamnan jihar Kano ya amince da wannan mataki na mataimakin nasa, sai kwamishinan ya ce: \”Mai girma gwamna na nazarin wannan takarda.\”

A baya-bayan nan ne mataimakin gwamnan ya rubuta wata wasika ga hukumomin tsaron Najeriya, inda yake neman da su dauki mataki a kan abin da ya kira wata barazana da jami\’an gwamnatin jihar Kano ke yi ga lafiyarsa.