Mutane 23 Sun Mutu Sakamakon Hadarin kwale- kwale A Jihar Sakkwato

0
475
Rabo Haladu Daga Kaduna
MUTANE 23 ne suka rasa rayukansu a daidai lokacin da suke kokarin tserawa daga wani
hari da ‘yan bindiga suka kai wa kauyukansu.
Mutanen sun hadu da ajalinsu ne lokacin da suke kokarin tsallaka wani kogi ta hanyar
amfani da kwale-kwale domin komawa a kauyukansu da suka baro biyo bayan hare-haren
da \’yan bindiga suka kai masu a kwanakin da suka gabata.
Lamarin ya faru ne a makwannan da muke ciki kuma mai magana da yawun rundunar \’yan sanda jihar Sakkwato DSP Codilian Wawei, ta shaida wa manema labarai  cewa, adadin mutane da ke cikin kwale-kwalen sun fi 50, kuma hatsarin ya faru ne a gundumar Gandi.
Tuni dai aka tabbatar da mutuwar mutane 23 a cewarta, an kwantar da wasu 8 a asibiti domin samun kulawa jami\’an kiwon lafiya yayin da ake ci gaba da neman wasu mutane 9.
Bayanai sun nuna cewa, mutum 17 daga cikinsu mata ne yayin da sauran 4 yara kanana ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here