Yarfe Da Karyar \’Yan Siyasa Ake Yadawa Kan Gwamna Tambuwal

  0
  537
  Gwamna Aminu Waziri Tambuwal sha kwaranniya

  Daga Wakilinmu

  HOTUNAN tawagar wasu motocin gwamnati ce (ba ta Sakkwato ba) aka tsinto ake yadawa ana cewa, Gwamnan na jihar Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya gamu da fushin matasa wadanda suka je tarbarsa suna ihun \’ba ma so, ba ma so\’, alhalin Gwamna Tambuwal yana kan hanyarsa ta dawowa daga Abuja zuwa Sakkwato ko tasowa bai yi ba, a lokacin da ake yada labaran da hotunan a kafafen yada labarai na zamani.

  Alhaji Tanimu Kyadawa ne yake wannan tsokacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Sakkwato, inda ya ce mutane su rika yin tunani kafin su yada kowane labari suka tsinta a kan hanya, domin kuwa za a shiga kage da karya tare da cin fuskar manyan jama\’a

  Daga nan ya ce, adawa a siyasa ba gaba ba ce ta dindindin, domin su \’yan siyasa ba sa jin kunyar su yaudarar da al\’umma musamman matasa, don haka a kiyaye a mayar da komai wajen Ubangiji Allah Mai yadda Ya so da bayinSa a lokacin da Ya so. Mai bada mulki ga wanda Ya so a kuma lokacin da Ya so.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here