APC Ta Shirya Ganin Fushin \’Yan Najeriya A 2019 – Sanata Hunkuyi 

  0
  582
  Usman Nasidi Daga Kaduna
  SANATA Suleiman Othman Hunkuyi mai wakiltan Kaduna ta Arewa ya ce jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kuntata wa \’yan Najeriya don haka ta shirya ganin fushin mutane a 2019.
  Ya bayyana hakan a bikin tarbar masu sauya sheka da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) babin jihar Kaduna ta shiya a harabar Trade Fair da ke Kaduna a ranar Litinin.
  Hunkuyi wanda ke maida martani a madadin saura masu sauya sheka ya ce \”Allah ke bayar da mulki amma gwamnatin APC a Kaduna da Najeriya ta kuntata wa jama’a don haka za su nuna fushinsu a lokacin da ya kamata.
  “Ba ma zagi amma muna fadin gaskiya. Ina fada wa El-Rufai ya yi amfani da lokacin da ya rage masa a kan mulki don hada kayyayakinsa sannan ya shirya barin gidan gwamnati.
  Ba ma zagi,amma suna jin ciwo ta hanyar fadin gaskiya da muke yi.\”

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here