Dalilin Da Ya Sa Mataimakina Ya Yi Murabus – Gwamna Ganduje 

0
593
Gwamna Abdullahi Ganduje
Daga Usman Nasidi
A RANAR Litinin, ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar mataimakinsa, Farfesa Hafiz Abubakar, ya yi murabus ne saboda tsoron za a tsige shi.
Kwamishin nan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ne ya sanar da hakan a wata takarda da gwamnatin jihar Kano ta rabawa manema labarai a Kano. Garba ya rawaito gwamna Ganduje na cewar Farfesa Hafiz ya yanke shawarar ajiye mukaminsa ne bayan ‘yan majalisar dokokin jihar Kano 30 daga cikin 40 sun fara yunkurin daukan matakan tsige shi.
Ya bayyana cewar za a tsige tsohon mataimakin gwamnan ne saboda wasu zarge-zarge na badakalar kudi da kuma kalamai da kan iya haifar da kiyayya tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC. A takardar tasa ta murabus, mai dauke da kwanan watan ranar 5 ga watan Agusta, Farfesa Hafiz ya bayyana cewar ya so ya zauna a ofis har zuwa karshen wannan zangon amma rashin sasanta wasu matsaloli tsakaninsa da gwamna Ganduje ya saka shi yanke shawarar yin murabus.
Ina mai matukar nadamar sanar da kai cewar na yanke shawarar ajiye mukamina daga ranar 4 ga watan Agusta, 2018.\”
\”Mai girma gwamna, na so zama tare da kai har zuwa karshen wannan zangon amma wasu rashin sasanta banbancen mu a kan sha\’anin mulki da gwamnati da kuma na kashin kai, ya saka ni jin cewar ban yiwa kaina da kai kan ka da jama\’ar jihar Kano adalci ba idan na cigaba da zama tare da kai a matsayina na mataimakin gwamnan jihar Kano,\” a cewar Farfesa Hafiz.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here