Ciwon Kafa Ya Kama Matashin Nan Da Ya Je Abuja A Kasa Dalilin Shugaba Buhari

0
582
Daga Usman Nasidi
A SHEKARAR 2015 ne Abubakar Duduwale, masoyin shugaba Buhari, ya taka da kafarsa daga Yolan jihar Adamawa zuwa Abuja domin ya halarci rantsar da Buhari.
Duduwale ya bayyana cewar ya yi tattakin ne domin nuna jin dadinsa da nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shekarar 2015, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa. Kafafen yada labarai da suka hada da gidan talabijin na kasa (NTA) sun nuna tattakin na Duduwale a ranar da ya bar Yola.
Duduwale, dan kabilar Chamba daga karamar hukumar Yola ta Arewa, ya fara tattakin na shi ne daga kofar garin Yola da ke kan babban titin Yola zuwa Numan da misalin karfe 6:30 na safe.
Shekaru uku bayan ya yi wannan bajinta, Duduwale ya gamu da lalurar ciwon kafa kamar yadda hotunansa da suka mamaye kafafen sada zumunta suka tabbatar.
Wani ma\’abocin amfani da shafin sada zumunta na Tuwita @GASSA01 ya saka hoton Duduwale tare da bayyana cewar yanzu haka ya nakasa kuma yana matukar neman taimako

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here