\’An Kora Mu Cikin Daji Kamar Shanu\’

0
662
Sun kashe, wasu kuma sun sha da kyar
Rabo Haladu Daga Kaduna
WANI da \’yan fashi suka sace ya zanta da manema ,  labarai inda ya bayyana yadda aka tare su a kan hanya sannan aka kora su cikin daji bayan an yi masu fashi.
Mutumin wanda aka tare shi yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Gusau ya ce \’yan fashin na amfani da wasu sautuka domin sadarwa a tsakaninsu.
\”Zan je Gusau, ina kan hanya kafin na kai Giwa, sai na ga mutane da kayan sojoji.\”
\”Sai muka ji an bude wuta ana ta harbi.\” \”Suna cewa tsaya ko in harbe ka.\”
\’Yan fashi sun \’kashe mutum 10\’. A cewar mutumin, an tare motoci da dama a
lokacin fashin, sannan an kwace masu kudade da wayoyinsu na hannu.
\”Bayan an gama fashin sai suka kora mu cikin daji suna dukan mu.\”
Ya tabbatar da cewa an kwashe kimanin minti talatin ana fashin ba tare da jami\’an tsaro sun kawo dauki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here