Ban San Inda Aka Samo Batun Ficewa APC Ba – Gwamnan Neja

  0
  616
  Sai A Tanaji Dokar Kasa!!!
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
  GWAMNAN Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa shi kansa bai San inda masu kokarin yada cewa wai zai fice daga cikin jam\’iyyarsa ta APC suka Samo asali ba.
  Abubakar Sani Bello da ake wa lakabi da (Abu lolo) ya tabbatar wa manema labarai cewa ko kadan ba a taba tuntubarsa da irin wannan zance ba Kuma ba su yi shi da kowa ba, amma abin mamaki sai ga wani yana tambayarsa game da irin wannan batu.
  \”Ni Ina daga cikin masu ba wadanda suka ce za su fice daga APC shawarar kada su aikata hakan, to ta yaya wani ko wasu gungun jama a za su rika yada irin wannan
  Ya ce a dai bari nan da dan lokacin kwanaki sati daya zuwa biyu aga abin da zai faru \”koda yake ni ba a bakina za a ji wannan maganar ba\”. Inji Gwamnan Neja.
  In dai za a iya tunawa batun ficewar jama\’a musamman Yan siyasa daga cikin APC ne ke mamaye sararin siyasar kasar nan don haka wadansu sai kawai su zabi wanda suka ga dama su makala masa batun ficewar kawai.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here