Kujerar Gwamna: Sani Sidi Ya Bayyana Sha\’awarsa

  0
  616
  Gwamna Malam Nasiru El-Rufa\'i na Jihar Kaduna
  Mustapha Imrana, Daga Kaduna
  TSOHON Daraktan janar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) Alhaji Sani Sidi Ya Bayyana sha\’awarsa ta neman kujerar gwamnan Kaduna a karkashin jam\’iyyar PDP.
  Alhaji Sani Sidi Ya dai bayyana hakan ne a wajen wani babban taron gangamin magoya bayansa da suka yi jerin Gwano zuwa Ofishin Jam\’iyyar reshen Kaduna.
   Lokacin wannan ziyara zuwa Ofishin Sani Sidi Ya Mika takardar bayyana sha\’awarsa ga shugabannin PDP na Kaduna karkashin jagorancin Mista Felix Hassan Hyat.
  \”Dalilin wannan ziyarar shi ne domin shaidawa jam\’iyya cewa Ina son yin takara karkashin jam\’iyyar PDP ashekarar 2019.
  Ya ci gaba da shaidawa dimbin jama\’ar cewa bukatar hakan ta taso ne bayan irin yadda Yan uwa da abokan arziki suka tattauna kuma suka yanke wannan hukuncin lallai sai a fito a nemi wannan kujera ta daya a Jihar Kaduna.
  Don haka ne muke neman addu\’o\’inku da sa albarka a wannan yunkurin da masu ruwa da tsaki suka amince a nema.
   \”Wannan yunkurin ba zai rasa nasaba da irin yadda nake bukatar ganin na ceto Jihar Kaduna daga halin da take ciki ba ta yadda za a Dora ta akan hanyar ci gaba kamar yadda za ta dace da tsarin duniya.
  A halin yanzu akwai wadansu mutanen da ba su da tausayin da suka jefa jama\’a cikin mawuyacin hali, duk da yanayin mutane ya yi tsanani amma su Babu ruwansu\”. Inji Sani Sidi.
  \”Irin abin da jama\’a suka taru suka zaba shi ne canji amma kuma madadin aga canjin ciyar da jama\’a gaba sai nutsewa ake yi cikin wani hali mawuyaci musamman ga Talakawa.
  \”A shekaru uku na wannan Gwamnati an samu matsalolin cin hanci da ba a taba samu ba a can baya a tarihin kasar nan don haka ni Ina kokarin kawo canjin ci gaban Jihar Kaduna ne da kasa baki daya, domin kada a bari komai a tabarbare baki daya\”. Inji Sani Sidi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here