BABU WATA BARAZANA DA PDP ZA TA YI WA LALONG A ZABEN 2019-USTAZ IBRAHIM

  0
  863
  Ustaz Ibrahim Barikin Ladi

  Isah Ahmed, Jos

  Ustaz Ibrahim Barikin Ladi shi ne sakataren kudi na jam’iyyar APC reshen jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa babu wata barazana da jam’iyyar PDP, zata yiwa gwamnan jihar Filato Simon Lalong da jam’iyyarsa ta APC,  a zaben shekara ta 2019 a jihar Filato.

   

  Ga yadda tattaunawar ta kasance

  GTK; A matsayinka na jigo a jam’iyyar APC reshen jihar Filato, ganin cewa zabubbukan shekara ta 2019 ya gabato, wanne hali kuke ciki?

  Ustaz Ibrahim; To zan iya cewa yanayin siyasa a jihar Filato, mu dai sai dai mu yiwa Allah godiya. Domin duk da ga zabubbukan shekara ta 2019 sun gabato, amma mu babu wani tsiko da muka samu a jihar nan.

  A kullum jam’iyyarmu ta APC, sai kara dinkewa take yi. Wasu  ‘yayan jam’iyyu suna ta ficewa daga jam’iyyunsu suna komawa wasu jam’iyyun, amma mu jam’iyyarmu ta  APC  a  jihar Filato, kullum sai kara shigowa ake yi.

  Kuma ‘yan takara suna ta  fahimtar juna, muna zama da su muna yin tarurruka,  a wurare daban daban na jihar nan. Halin da muke ciki ke nan a jihar Filato.

  GTK; Ganin irin adawar da jam’iyyar PDP take nuna  maku  da kuma irin shirye shiryen da suke yi,  na tunkarar zaben shekara ta 2019 baka ganin zasu iya kwace wannan jiha daga jam’iyyarku ta APC?

  Ustaz Ibrahim; Idan ka dubi yanayin yadda  jam’iyyar APC take mulki jihar Filato. Tun daga lokacin da aka kafa wannan jiha.

  Ba a taba samun lokacin da ma’aikatan jihar nan suke  samun albashinsu a kan kari, kamar a wannan  lokacin da  jam’iyyar APC take mulki ba.

  Kuma ana ganin ayyukan raya kasa suna tafiya ko’ina a wannan jiha, wasu ayyukan  tun zamanin mulkin damakoradiya na baya aka fara, amma  wannan gwamnati ta APC  ta sanya aka cigaba da wadannan ayyuka. Tun daga kananan hukumomi har zuwa jiha. An  baiwa kantomomin kananan hukumomi umarnin su kammala irin wadannan ayyuka.

  Bayan haka idan ka duba a cikin jam’iyyar APC a  jihar Filato akwai wasu tsuraru wadanda basu zabemu ba, a zaben da ya gabata. Amma yanzu sun  dawo jam’iyyar APC. Don haka mu  karuwa muka yi a jam’iyyar APC a jihar Filato.

  Saboda haka babu wata barazana da PDP zata yiwa jam’iyyar APC a jihar Filato.

  GTK; Wato a ganin ka gwamna Lalong zai iya cin zaven shekara ta 2019?

  Ustaz Ibrahim; Kwarai da gaske Lalong zai iya cin ye zaben shekara ta 2019. Don haka mu yanzu ma, muna tunanin ayyukan raya kasa da muka sanya a gaba a shekara ta 2019, domin mu zaben shekara ta 2019 ba damuwarmu ba ce. Domin Lalong zai ci zabensa, saboda irin yadda yake tafiyar da mulkin jihar nan.

   

  GTK; Ganin irin yadda wasu matasa suka je suka yi zanga zanga a gidan gwamnatin jihar nan da kuma jifan tawagar gwamna Lalong da aka yi   kwanakin baya, baka ganin wannan wata alama ce  da take nuna cewa akwai matsala kan sake zaben Lalong?

  Ustaz Ibrahim; Wannan ba wata matsala bace domin idan ka dubi wadanda suka yi zanga zangar  nan da kuma wadanda suka jefi tawagar gwamna ba wadanda suka mallaki hankalinsu bane, bata gari ne.

  GTK; Wasu shugabannin wannan jam’iyya ta APC da wasu da suka yiwa wannan jam’iyya aiki a nan jihar Filato, suna ta koke koken cewa su har yanzu basu ci gajyar wannan jam’iyya ba, an yi watsi da su?

   

  Ustaz Ibrahim; Idan wani shugaba a wannan jam’iyya ta APC a nan jihar Filato, ya ce bai ci gajiyar wannan jam’iyya ba, abin ya kan bani dariya. Irin wadannan mutane ba ‘yan asalin jam’iyyar APC bane. Amma dan jam’iyyar APC na asali ya san cewa abin da muka hori kawunanmu da shi, shi ne yaki da cin rashawa da rashawa. Kuma  ba a kafa jam’iyyar APC don a debi kudin gwamnati a rabawa ‘yayan jam’iyya  ba. Gwamnatocin baya sukan debi kudin gwamnati  su rabawa ‘yayan jam’iyya. Don haka ada an saba da  facaka  da kudin gwamnati. Wannan gwamnati ta hana facaka da kudin gwamnati.

  Misali  kamar ada a jihar nan, daga gidan gwamnati  an je ofishin hukumar alhazai na jihar nan,  an kwashe kudaden da alhazai suka biya don tafiya aikin hajji.

   Sai da wannan gwamnati ta biya kudaden kujerun alhazai sama da 600 da aka kwashe aka cinye, a zamanin gwamnatin da ta gabata. Mu ba zamu yarda da irin haka ba, a zamanin wannan gwamnati.

  GTK; Wani abu da aka dade ana ta magana a jihar nan, shi ne zaben shugabannin kananan hukumomi shin  wai yaushe ne za a yi wannan zabe?

  Ustaz Ibrahim; Zaben kananan hukumomi bai gagara ba a jihar Filato. Sai dai ya kamata a fahimci cewa wannan zaben kananan hukumomi, za a yiwa jama’a ne. Don haka a duk lokacin da aka ce ana yiwa jama’a  wani abu, ya kamata ayi tunani  kafin a aikata wannan abin. Wato a takaice wannan gwamnati ta jihar Filato tana kokarin dawo da zaman lafiya ne a jihar nan. Muna son zaman lafiya ya dawo ne kafin mu gudanar da wannan zabe.

  Domin ba zai yi kyau ba, ace ana kashe kashe wasu sun rasa muhallansu  ace za a gudanar da zabe a wannan hali.

  Ganin cewa ba dukkan kananan hukumomin jihar nan ake rikici ba. Nan bada daewa ba, za a zabi kananan hukumomin da ba a rikici, a fara gudanar da zaben, kafin azo ayi a kananan hukumomin da ake rikici, bayan an sami zaman lafiya.

  Yanzu idan ka duba kamar kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom da Jos ta kudu akwai ‘yan gudun hijira da suke gudun hijira a wurare daban daban. Mai girma gwamna ya nada kwamitin sake zaunar da irin wadannan ‘yan gudun hijira. Sai  an  sami zaman lafiya a zaunar irin wadannan ‘yan gudun hijira kafin azo a gudanar da wannan zabe.

   

  GTK; Wanne sako ne kake da shi zuwa ga al’ummar jihar Filato?

  Ustaz Ibrahim; Sakon da nake son na mika ga al’ummar jihar Filato shi ne ya kamata mu fahimci cewa zaman lafiya yafi zama dan sarki. Kuma mu yi imanin cewa Allah  ne ke da mulki kuma shi ne yake bada shi ga wanda yaso, kuma  yake karbewa a hanun wanda yaso. Don haka mu yi hakuri mu zauna da junanmu  lafiya kuma mu baiwa gwamnati hadin kai. Idan muka baiwa gwamnati hadin kai duk abubuwan more rayuwa da muke bukata zamu samu.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here