Guguwar Sauyin Sheka: Tsohon Mukaddashin Gwamna A Arewa Ya Fice Daga Jam\’iyyar APC

  0
  569
  Daga Usman Nasidi
  TSOHON mukaddashin gwamna a jihar Adamawa dake a arewacin Najeriya kuma na hannun gwamnan jihar Umaru Jibrilla mai suna Ambasada James Barka ya sanar da ficewar sa daga jam\’iyyar All Progressives Congress (APC).
  Rahotanni da muke samu na bayyana cewa shi dai Mista Barka tsohon Ambasada ne na Najeriya a kasar Malaysia kuma mamba ne a kwamitin shugaban kasa na farfado da yankin arewa ta gabas.
  Da yake tabbatar da ficewar tasa daga jam\’iyyar, Mista Barka ya bayar da dalilai na rashin kyautawar gwamnan jihar da kuma rashin gaskiyar da ake tafkawa a gwamnatin a matsayin musabbabin ficewar ta sa.
  A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Benue dake a arewacin Najeriya ya bukaci shugaban jam\’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole da ya fito bainar jama\’a ya bashi hakuri tare da neman gafarar sa game da kazafin da yayi masa a cikin kwanaki bakwai ko kuma ya kai shi kotu.
  Gwamna Ortom dai yayi wannan kiran ne ga shugaban jam\’iyyar ta hanyar wata takarda da lauyoyin sa suka rubuta, suka kuma rabawa manema labarai a ranar 6 ga watan Agusta.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here