Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Hanyar Gadar Kawo A Kaduna

0
768

 

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

 

SAKAMAKON irin yadda ruwan sama da aka yi a Daren ranar lahadin data gabata kamar da bakin kwarya a halin yanzu Gadar sama da ke a dai dai Tashar Motar kawo a halin yanzu masu bi ta kasan Gadar na fuskantar bazanar ruwa ta hana su wuce wa.

 

Tsakanin haka ne yasa muke sanar da masu shigowa cikin garin Kaduna a manyan motoci da kanana da su yi hankali saboda ruwan sama ya Mamaye hanyar kasan Gadar musamman masu zuwa Abuja da Unguwannin kawo da Bakin ruwa da Hadin ruwa Rigasa Kaduna da kuma Sabon Tasha, unguwar Romi har chukun da Kajuru da sauran su.

 

Dalilin wannan sanarwa shi ne na farko akwai matsanancin jerin Gwanon motocin da ya wuce kasuwar duniya idan mutum zai shigo garin Kaduna

 

A binciken da muka yi a wurin ya tabbatar mana cewa akwai hanyar ruwa dai dai kasan Gadar da aka fi Sani da kwalbatin da ake zuba shara ake konawa a kullum wannan ne yasa hanyar ruwan ta toshe, kamar yadda ma\’aikatan hukumar da ke aikin bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) suna tabbatar wa wakilin mu da ya halarci wurin.

 

Kamar yadda suka ce ( Mutane ne mun yi ta gaya masu cewa su daina zuba shara a wannan wuri amma sun ki kullum sai zuba wa suke yi, ga kuma irin matsalar da abin ya kawo

 

Faruwar wannan lamari da ke hana motocin fasinja da kuma na daukar kaya wuce wa da sauri, lamarin da a halin yanzu idan kananan motocin daukar kaya da na fasinja za su wuce ta bangaren hanyar kasan Gadar Kawo sai ruwan ya rike su har su mutu a cikin ruwan.

 

Suma manyan motocin Tirela ne kawai ke samu hanzarin wucewa da karfin gaske idan sun sa Giya da sauri.

 

Lamarin dai ya haifar wa mutane barin motocin da suke a ciki domin yin tafiyar kasa har su kawo inda ake daukar fasinja a kasan  Gadar kawo, kasancewa sai mota ta kwashe sama da awa daya bata ma iso wurin da ruwan ya tsare Gadar ba, wasu motocin kum suna mutuwa a kan hanya lamarin dai na neman zama wani Abu daban kasancewar hanyar ita ce sananniyar hanya ta shiga cikin garin Kaduna da Jihohin Arewa maso Yamma har ma daga kasashen Makwabtan Nijeriya.

 

A halin da ake ciki ma wadansu shaidun Gani da Ido sun shaidawa wakilinmu cewa tun a Daren jiya ma lokacin da ake ruwan saman har saman Gadar ya hauro

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here