MUTANEN AREWA BASU TABA ROKON BUHARI YA YI MASU AYYUKAN RAYA KASA BA – SALE BAYARI  

0
625

 

Isah Ahmed, Jos

 

SHUGABAN kungiyar cigaban al’ummar Fulani makiyaya ta Nijeriya Alhaji Sale Bayari, ya bayyana cewa shi bai taba ganin inda mutanen Arewa suka zauna da shugaban kasa Muhammad Buhari, suka roki ya yi masu wasu ayyukan raya kasa kamar hanyoyi mota ko asibitoci ba.

Alhaji Sale Bayari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron karramar da kungiyar daliban manyan makarantun arewa suka yi masa da Garkuwan matasan Arewa, a garin Jos babban birnin jihar Filato a karshen makon da ya gabata.

Ya ce “a  kullum mutanen yankin  Neja Dalta suna cewa ayi masu kaza, ayi masu kaza kuma su ce idan ba a yi masu ba, ba za a dauki mai ba.”

Amma mu mutanen Arewa bamu taba cewa idan ba a yi mana kaza ba, ba za a dauki masara da tumatur da shanu daga Arewa a kai kudu ba.

‘’A yankin Neja Delta akwai mutanen da basa aikin komai, amma in wata ya kare ana baiwa kowa Naira dubu 65. Amma a arewa akwai miliyoyin mutane da suke son a dauke su aikin da za a rika basu naira dubu 18, a wata.

Acewarsa, yanzu idan aka je Ibadan za a ga hanyar mota da ake yi, hakazalika a garin Asaba akwai gadar da ake yi. Ana yi masu irin wadannan ayyuka ne saboda suna nema ayi masu.

Ya kara da cewa ya kamata mutanen arewa su rika fitowa suna mika bukatun abubuwan da suke son a yi masu, kana Shima shugaban Buhari ya kamata ya san cewa mutanen arewa suna son sa, ta hanyar yi masu wasu abubuwa na cigaba.

A karshe ya bayyana mamakinsa ga wannan kungiyar ta yadda aka yi suka san shi kuma suka san abubuwan da yake yi, har suka karrama shi da Garkuwan matasan Arewa, don haka ya yi godiya akan wannan karramawa da aka yi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here