YIN BABBAR SALLAH RANAR TALATA A NIJERIYA  DAIDAI NE-SHEIKH SA’IDU JINGIR

0
790

 

 Isah  Ahmed, Jos

 

SA’I na kasa kuma mataimakin shugaban majalisar malamai na biyu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah ta qasa, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana cewa yin babbar sallah ranar talata a Nijeriya dai dai ne, domin za ayi hawan Arfa ne a ranar litinin.

Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce makkah ita ce cibiyar musulunci ta duniya kuma ba zai yiwu ba ace an yi Arfa kuma limamin duniya ya yi huduba kuma an gayawa musulmi cewa ranar Arfa ce wato 9 ga wata, kana ranar idin babbar sallah sannan a wayi gari wata kasa da take da’awar musulunci, su ce ba zasu yi aiki da wannan sanarwa ba.

Jingir ya yi bayanin cewa wani abu ne ake samu a kasarmu Nijeriya, wanda  idan aka samu labarin cewa Saudiya sun ga wata, mu kuma nan Nijeriya sai ayi fatawa da ka.

Ya ce mun sha tattauna wadannan abubuwa a wuraren tarurrukan da muke yi a Nijeriya. Mun ja hankalinsu kan cewa a ka’idar shari’a idan aka ce gabashin duniya taga wata, to yammacin duniya duk wadanda labari ya riske su, zasu yi lissafi da wannan ganin wata.

“Tilas ne mu bi lissafin Saudiya mu yi watsi da lissafin kasarmu saboda haka sai muyi idin babbar sallah a ranar talata washe garin ranar litinin idan an yi Arfa na duniya.”

Wanda kuma Allah ya basu iko su yi azumin ranar Arfa wanda Manzon Allah SAW ya ce yana kankare zunubi na shekara guda da watanni shidda ga wanda bai sami tafiya aikin hajji ba. Kaga bai yiwuwa ace zamu canja lissafi ya kasance bamu sami yin wannan azumi ba. Wannan al’amari yana nan yadda yake abin da Nijeriya tayi na cewa ayi sallah ranar talata ya yi daidai’’.

Sheikh Sa’idu ya bada tabbacin cewa idan suka je Saudiya aikin hajji, tun da yanzu suna kan hanya zasu yi magana da hukumomi a can kan wannan al’amari kuma idan Allah ya basu ikon dawowa gida Nijeriya bayan sallah zasu kai ziyara ga mai alfarma Sarkin musulmi su jawo hankali cewa a kirawo malamai azo a zauna a tattauna a kawo mafita kan wannan al’amari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here